Bidiyo da hotunan faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn

Bidiyo da hotunan faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi ya lashi takobin gano inda mutane suka kai dukiyoyin gwamnati

- A ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba suka damki wani fasto da kayan amfanin asibiti kimanin na Naira biliyan 1.2

- Bayan damkarsa ne ya kasa bayani a kan yadda aka ga kayan a bayan motarsa da ya boye a wani daji kusa dasu

'Yan sandan jihar Kogi sun kama wani Fasto mai suna Sunday Edino da laifin satar kayan amfanin asibiti, wadanda za su kai kimanin Naira Biliyan 1.2.

KU KARANTA: Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3

Bidiyo da hotuna faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn
Bidiyo da hotuna faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn. Hoto daga @LindaIkejiblog
Asali: Twitter

An kama faston ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, bayan kwamishinan 'yan sandan jihar, da yaransa sun bi gida-gida suna binciken kayan da matasa suka sata da sunan zanga-zangar EndSARS.

Bidiyo da hotuna faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn
Bidiyo da hotuna faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Bayan an kama shi, Edino ya kasa amsa tambayoyi a kan kayan amfanin asibiti da aka gani a bayan motarsa da ya boye a dajin da ke kusa da su, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya sabunta nadin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Bidiyo da hotuna faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn
Bidiyo da hotuna faston da aka kama da kayan asibiti na sata masu darajar N12bn. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

A wani labari na daban, babban birnin jihar Kogi, Lokoja ya koma kamar filin daga a ranar Lahadi da daddare, bayan bata-garin da suka je sato kayan tallafin COVID-19 sun gamu da jami'an tsaro masu kulawa da kayan ADP da ma'adanar kamfanoni masu zaman kansu.

Jami'an tsaron sun gamu da bata-garin da suka kwaso taki da shinkafa. Sakamakon gumurzun, mutane 4 ne suka rasa rayukansu, sai mutane 30 har da wani dan jarida da suka ji munanan raunuka.

Shigen lamarin da ya faru a Kogi, ya maimaita kansa a Calabar da Cross River, inda fiye da mutane 10 suka rasa rayukansu, ciki har da wata mata mai juna biyu, inda aka yi ta tafka gumurzu tsakanin bata-gari da jami'an tsaro tun ranar Asabar har Lahadi da daddare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel