Hukumar NSCDC ta sallami hafsan da aka gani a bidiyo yana wawason kayan abinci a Abuja (Bidiyon)

Hukumar NSCDC ta sallami hafsan da aka gani a bidiyo yana wawason kayan abinci a Abuja (Bidiyon)

- Jami'in NSCDC ya rasa aikinsa sakamakon satan kayan abincin COVID-19 a Abuja

- A ranar Litinin bata gari suka fasa runbun abinci a unguwar Gwagwalada sukayi wawason kayan hatsi

- Wasu sun dauki bidiyon hafsan NSCDC yana daukan nasa rabon

Hukumar tsaron farin hula watau Sibil Defens ta sallami wani hafsan ta, Iliya Ibrahim, daga aikin bayan bayyanar bidiyon dake nuna shi ya saci kayan abinci yayinda matasa suka fasa rumbun abincin tallafin Korona a unguwar Gwagwalada Abuja.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an ga Iliya Ibrahim sanye da kayan aiki ya debi wasu kayan abinci lokacin da matasa ke wawaso.

Sallamar Ibrahim na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban hukumar, Ekunola Gbenga, ya saki ranar Talata.

Jawabin na dauke da take 'NSCDC ta sallami hafsan kan laifin sata a Abuja.'

Wani sashen jawabin yace: "Kwamanda Janar, Abdullahi Gana Muhammadu ya amince da shawarar kwamitin ladabtar da kananan hafsoshi na sallamar Iliya Ibrahim na Gwagwalada kan hada kai da matasa wajen satan kayan tallafin COVID-19 a wani runbun abinci."

KU DUBA: Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: An fara wahalan man fetur a Najeriya, NNPC ya ce laifin #EndSARS ne

A wani labarin, ana tsaka da raba kayan tallafi a ranar Litinin wasu bata-gari suka dakatar da lamarin, daganan suka kwashe kayan tas sukayi awon gaba dasu.

Sakamakon labaran jihohin da suka yi ta satar kayan tallafi, sai gwamnatin jihar ta yanke shawarar raba kayan abincin kananan hukumomin da aka ajiye kayan tallafinsu a Ijebu, wadanda suka hada da karamar hukumar Ode, Sagamu da Ifo.

Masu rabawar da suka taru a Ijebu, sun fara raba kayan abincin kenan sai ga bata-garin, wadanda suka kwashe kayan tallafin suka kara gaba.

Hukumar NSCDC ta sallami hafsan da aka gani a bidiyo yana wawason kayan abinci a Abuja (Bidiyon)
Hukumar NSCDC ta sallami hafsan da aka gani a bidiyo yana wawason kayan abinci a Abuja (Bidiyon) Hoto: Jami'an NSCDC
Asali: Depositphotos

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel