EndSARS: Legos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna
- An lalata motocin BRT da dama a Lagos ranar Talata, 27 Oktoban shekarar 2020
- Yan tawayen sun aikata barnar tasu a Mil 2 wani bangare na jahar ta Legas
- Rahotanni sun bayyana cewa a fasa shaguna da kantina da dama a yankin
Ga dukkan alamu yan tawaye a Legas basu gama da lalata kayayyaki ba inda suka waiwayi yankin Mil 2 suka kuma ci gaba da barna a ranar Talata 27 ga Oktoba a yankin da ke jihar Legas.
A wani rahoto mai ban tsoro da PM News ta fitar ya nuna cewa wasu gungun 'yan daban sun lalata da yawa daga cikin motocin BRT kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
![EndSARS: Lagos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna EndSARS: Lagos ta sake rikicewa yayin da yan tawaye suka lalata motocin BRT, suka fasa shaguna](https://cdn.legit.ng/images/1120/bd8a8c4799ce7e48.jpeg?v=1)
Asali: UGC
DUBA WANNAN: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona
An kuma hango su da adduna suna fashe shaguna a yankin inda rikicin ya barke har Owade axis kan hanyar Ikorudu.
Wannan ya tilasta Primero, mai kula da motocin BRT fara tunanin dakatar da da al'amura saboda gudun kada a ci gaba da lalata musu motoci.
Sai dai kuma, wani jami'in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa yan jarida cewa tuni aka girke jami'an yan sanda a yankin don saita al'amura da dawo da zaman lafiya.
KU KARANTA: Abin da yasa muka jinkirta rabon tallafin korona a Sokoto - Gwamna Tambuwal
A makamancin hakan, wasu fusatattun matasa sun sauke fushinsu akan gwamnan jihar, Babajide Sanwa-Olu.
Matasan kamar yadda jaridar This Day ta rawaito, sun cinna wa gidan mahaifiyar Sanwa-Olu wuta ranar Laraba 21 ga Oktoban 2020.
A wani labarin dabam, nn sace ma'aikacin jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse (FUD), jihar Jigawa mai suna Shehu Abdulhamid a jihar Kano kamar yadda LIB ta ruwaito.
Mai magana da yawun jami'ar, Abdullahi Bello ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a 23 ga watan Oktoban shekarar 2020.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng