Mutum 13 ne suka rasu a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna

Mutum 13 ne suka rasu a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna

- Mummunan hadarin mota ya jawo mutuwar mutane da dama a hanyar Kaduna zuwa Kano

- Wata babbar motar fasinja ce ta kwace ta daki motoci hudu lamarin da ya haddasa Mummunan hadari.

- Hukumar FRSC ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma tabbatar da adadin wanda abin ya shafa

Akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin mota daya faru a babban titin Kaduna zuwa Kano a cewar rahoton da The Nation ta wallafa.

Wasu daga mafi yawan fasinjoji kuma suka ji raunika a hadarin wanda ya hada da babbar motar daukar fasinja da wasu motoci guda hudu.

Mutum 13 ne suka mota a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna
Mutum 13 ne suka mota a hadarin mota a babban titin Kano zuwa Kaduna. Hoto daga The Nation Ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

Wakilinmu ya rawaito cewa hadarin ya faru a dai dai wani kauye da ake kira Jar-marmara a karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna.

Wani wanda ya shaida al'amarin Mallam Sani Haruna, ya bayyana 6: "babbar motar ce ta kwace ta kuma daki motoci hudu, inda mutum 16 suka mutu nan take. Motoci hudun duka sun lalace".

An rawaito cewa babbar motar ta taso ne daga Lagos inda ta nufi Kano da yammacin Litinin kafin hadarin ya faru da safiyar Talata tafiya kadan kafin zuwa inda ta nufa.

KU KARANTA: Abin da yasa muka jinkirta rabon tallafin korona a Sokoto - Gwamna Tambuwal

Majiyarmu ta gano cewa da yawan wanda suka ji rauni an garzaya dasu asibiti don basu kulawa.

Babban jami'in FRSC mai kula da jihar Kaduna, Hafiz Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma tabbatar da adadin wanda abin ya shafa.

A wani labarin, an ruwaito cewa mutum biyar sun rasu yayin da suka ƙoƙarin rabon wani adadin kudi da suka tsinta a maj'ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen sun ɓalle wurin ajiyar abincin ne inda suka tsinta jakuna biyu ɗauke da kuɗi ƴab dubu-dubu kusa da sakatariyar Kungiyar Kirista ta Najeriya a Jalingo ranar Asabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel