An fara wahalan man fetur a Najeriya, NNPC ya ce laifin #EndSARS ne

An fara wahalan man fetur a Najeriya, NNPC ya ce laifin #EndSARS ne

- Mazauna birnin tarayya sun waye gari babu man fetur a gidajen mai

- Wakilin Legit ya gano cewa tun ranar Asabar aka fara rashin mai a Abuja

- Idan aka kara yan kwanaki a haka sauran jihohin Najeriya zasu fara fuskantar haka

Ana fuskantar matsalar rashin man fetur a Birnin Abuja da ma kewayenta yayinda gidajen mai suke cike makil da dogon layi na ababen hawa a babban birnin tarayyar ranar Talata.

kamfanin man fetur na kasa, NNPC ta zargi zanga-zangar ENDSARS akan matsalar, amma tana fatan daga baya dogon layin man zai sassauta daga baya ranar Talatar.

Mai magana da yawun kamfanin, Dr Kennie Obateru yace da yawa daga cikin yan kasuwa suna samun man kuma zaa samu daidaito a matsalar man nan ba da dadewa ba.

Har ila yau, Daily Trust's ta gano cewa akwai matsaloli a cikin wasu daga cikin gidajen saida man fetur a birnin Abuja a ranar Talata.

A gidan man NNPC dake central area, Abuja, motoci da yawa suna ta kokarin shiga gidan man amma yar karamar kofa ce aka bude wacce mota daya ke shiga a lokaci daya.

DUBA NAN: Gwamnatin Saudiyya ta yi Alla-wadai da shugaban kasar Faransa

Rashin man fetur- NNPC ta zargi zanga-zangar ENDSARS
Rashin man fetur- NNPC ta zargi zanga-zangar ENDSARS
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Matasa sun ɓalle daƙin ajiyar kayan abinci a Niger, sun fara warwaso

Kazalika gidan man fetur na TOTAL dake Area 11 , yan bunburutu sun mamaye wurin yayinda suke saida shi da tsada.

Suna siyar da 4L akan N1000 zuwa N1200.

Sai kuma gidan mai na Rano da NIPCO dake Jabi, shima an fuskanci hakan kamar yadda wakilin Daily Trust ta ruwaito.

Zanga zangar ENDSARS ta fara cikin lumana amma ta sauya salo zuwa tashin hankali yayinda ake ta kona ofisoshin yan sanda da sace sace a shaguna.

Kazalika dakin ajiyar kayan tallafin COVID-19 ana ta fasawa ana sace sace.

Amma kungiyar yan kasuwan man fetur basu ce komai ba akan matsalar man fetur din.

A bangare guda, shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya umarci kwamandojin rundunar soji da su dakatar da masu satar dukiyoyin gwamnati da na jama'a a cikin kasa.

Ya umarcesu da su yi gaggawar dakatar da duk wata baraka a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel