Abin da yasa muka jinkirta rabon tallafin korona a Sokoto - Gwamna Tambuwal

Abin da yasa muka jinkirta rabon tallafin korona a Sokoto - Gwamna Tambuwal

- Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ya bayyana dalilin da yasa aka samu jinkirin rabon talatin korona a jiharsa

- Tambuwal ya ce ministan ma'aikatar Jinƙai da kare bala'i, Sadiya Umar ce ta umurci da dakata sai ta zo za a fara rabon kayan

- Gwamnan ya kuma ce tallafin da wasu masu taimako suka bayar suma sun umurci sai kayan ya taru kafin a fara rabon

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya musanta cewa ya ɓoye kayan abinci na tallafin korona yayin annobar.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya ke yi wa ƴan jihar jawabi kan zanga-zangar EndSARs da wasu ke yi.

Dalilin da yasa muka jikirta rabon tallafin korona - Tambuwal
Dalilin da yasa muka jikirta rabon tallafin korona - Aminu Tambuwal. Hoto daga Premium Times Ng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abinda yasa ba mu janye yajin aiki ba - ASUU

Ya ce zanga-zangar ya rikiɗe ya zama satar kayayyakin abinci da ake zargi na tallafin korona ne a cewar rahoton Premium Times.

"Jihar Sokoto ba ta ɓoye kayan abincin tallafin korona ba.

"Ba a yi zanga-zanga ba kuma ba samu tashin hankali da rikici ba," in ji Tambuwal.

A cewarsa, jihar ta samu tallafin korona kashi biyu sun barƙewar annobar.

"Akwai guda ɗaya wanda gammayar masu bada tallafin korona (CACOVID) suka bayar.

"An ji jinkirin rabar da wannan da watanni don wadanda suka bada tallafin suna son sai kayan sun taru.

"Bayan kammala tattarawar, mun raba kayan ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayyar jiha, Alhaji Sa'idu Umar.

"Na biyun kuwa wanda gwamnatin tarayya ƙarƙashin ofishin ministar jin ƙai da kare afkuwar bala'i, Sadiya Umar ta bayar.

DUBA WANNAN: Ministan Abuja ya kira taron tsaro na gaggawa

"Mun samu kayan ranar 17 ga watan Oktoba kwanaki 9 da suka wuce. Jinkirin da aka samu daga ofishin ministan ne.

"Tana son sai ta zo da kanta sai a fara raba kayan a gabanta. Ta nemi a jikirta har sau biyar kafin ta iso.

"Saboda haka ba laifin mu bane kuma har yanzu ana rabon kayan. Ministan ce ta ce mu dakata har sai ta zo. Abinda ya faru kenan," a cewar Tambuwal.

Gwamnan ya yi kira da al'ummar jihar su bawa masu rabon kayan abincin haɗin kai.

A wani labarn, an ruwaito cewa mutum biyar sun rasu yayin da suka ƙoƙarin rabon wani adadin kudi da suka tsinta a maj'ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen sun ɓalle wurin ajiyar abincin ne inda suka tsinta jakuna biyu ɗauke da kuɗi ƴab dubu-dubu kusa da sakatariyar Kungiyar Kirista ta Najeriya a Jalingo ranar Asabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel