An sace babban basarake har fadarsa a kan rikicin sarauta na shekaru 27

An sace babban basarake har fadarsa a kan rikicin sarauta na shekaru 27

- Wasu matasa sun shiga fadar sarkin Ikire da karfi da yaji sun sace sarkin

- Sun fatattaki fadawan da suka samu a fadar, tare da tayar da tarzoma

- Matasan sun ce sun yi amfani da lokacin EndSARS ne don tsige sarki

Wasu matasa sun shiga fadar sarkin Ikire, Oba Olatunde Falabi inda suka sacesa.

Daily trust ta gano cewa matasan sun gaji da zamansa a mulki na tsawon shekaru 27, shiyasa suka yi amfani da lokacin EndSARS din nan don su huce fushinsu.

Miyagun matasan sun fatattaki fadawansa daga fadar, kafin su dauke shi.

Faruwar lamarin ya tayar da hankulan mutane musamman mazauna kusa da fadar.

Matasan sunce kotun koli ta soke nadin sarkin tun 1993.

A 2014, Tsohon alkalin kotun koli, Alkali Walter Samuel Onnoghen ya soke nadin Oba Falabi a matsayin sarkin Ireland.

Tsohon gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, ya so yayi amfani da hukuncin kotun koli, amma abin ya ci tura, inda sarkin ya garzaya babbar kotu.

Babbar kotu kuma ta yi hukuncin da yayi daidai da ra'ayin sarkin.

KU KARANTA: Wawushe dukiyoyin jama'a : 'Yan sanda sun damke mutum 224 a jihohi Kwara da Cross River

An sace babban basarake har fadarsa a kan rikicin sarauta na shekaru 27
An sace babban basarake har fadarsa a kan rikicin sarauta na shekaru 27. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ana tsaka da rabon tallafin korona, 'yan daba suka buga wawaso

A wani labari na daban, Teslim Folarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya, ya ce karnukansa duk suna cikin keji ne, lamarin da yasa basu yagalgala naman wadanda suka kai farmaki gidansa ba a ranar Asabar.

Fiye da babura 250, firji 400, janareto 35 aka kwashe a gidan sanatan wadanda aka ware domin karfafa matasa a mazabarsa.

A tattaunawar da yayi da Dele Momodu a ranar Lahadi, Folarin ya bayyana mamakinsa a kan wannan harin, The Cable ta wallafa.

Ya ce yana shirin rarraba kayan ne ga jama'ar yankinsa wadanda suka sace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel