Da duminsa: Matasa sun banka wa gidan rediyo wuta a jihar Taraba

Da duminsa: Matasa sun banka wa gidan rediyo wuta a jihar Taraba

- Fusatattun matasa a ranar Litinin sun yi watsi da dokar kullen da aka saka a garin Jalingo na jihar Taraba

- Sun kutsa babban gidan rediyon gwamnatin jihar inda suka kwashe kayayyaki tare da lalata wasu

- Kamar yadda kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar yace, wannan babban abun takaici ne da tashin hankali

Daruruwan matasa a ranar Litinin sun yi watsi da dokar ta-bacin da aka saka a Jalingo, sun kutsa tare da tarwatsa kayayyakin aiki na gidan rediyon jihar.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Danjuma Adamu, wanda ya ziyarci gidan rediyon jihar, ya duba farfajiyar tare da ganin irin barnar da aka yi da kuma kushe lamarin.

Kwamishinan ya ce wannan barnar ta zarce zanga-zangar kawo karshen SARS da matasan suka fake da yi, Vanguard ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, matasan bata-garin sun yi awon gaba da duk wasu kayayyakin da za a iya dauka. Sauran kuwa sun lalata su saboda tsabar mugunta.

A yayin zantawa da manema labarai wurin duba barnar, Adamu ya ce lamarin da ya faru a cikin kwanaki biyun abun takaici ne.

"Daga fara fasa gidajen adana tallafin korona sai suka zarce zuwa fasa gidajen jama'a, shaguna, makaratun kudi ana kwashe musu kayayayaki," yace.

Ya kwatanta lamarin da abun tashin hankali domin kuwa an mayar da gidan rediyon tamkar kango.

KU KARANTA: Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Da duminsa: Matasa sun banka wa gidan rediyo wuta a Taraba
Da duminsa: Matasa sun banka wa gidan rediyo wuta a Taraba. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

A wani labari na daban, Rundunar 'yan sandan jihar Kwara a ranar Litinin ta tabbatar da kamen mutum 144 da ke da alaka da satar kayan gwamnati da na jama'a a Ilorin da ke jihar Kwara.

Bata-gari da suka boye karkashin inuwar masu zanga-zangar EndSARS a Ilorin a ranar sun dinga satar kayayyakin shaguna da na ma'aikatu. Sun dinga cin zarafin masu ababen hawa da kuma mazauna birnin.

A yayin zantawa da manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kayode Edbetokun, ya ce sun yi kamen ne bayan kokarin jami'an tsaro na hadin guiwa a jihar, The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel