Minista Sadiya Farouk ta yi martani bayan 'yan Najeriya sun bukaci ta yafe musu

Minista Sadiya Farouk ta yi martani bayan 'yan Najeriya sun bukaci ta yafe musu

- Ministan ma'aikatar tallafi da jin kan 'yan kasa, ta ce tana sane da irin zargin da ake mata tare da zagi

- Ministan ta ce ta yafe wa jama'a tunda sun gane kuskurensu kuma gaskiya ta bayyana karara

- Sadiya Umar Farouk ta yi jawabi ga manema labarai a kan zargin da aka dinga mata na rub da ciki a kan dukiyoyin tallafi

Ministan ma'aikatan tallafi da jin kan 'yan kasa, Sadiya Umar Farooq ta ce ta yafe wa duk wadanda suka zargeta da boye tallafin rage radadin korona wanda aka ware domin talakawan Najeriya.

Ta sanar da hakan ne yayin amsa tambayoyin manema labarai a Gusau a ranar Litinin da ta gabata, Vanguard ta ruwaito.

"Ina sane da irin zargina da zagi da jama'a ke yi tare da ma'aikatata a kan kayan rage radadi da gwamnatin tarayya ta bayar.

"Ina yawan sanar da cewa ina kokarin sauke nauyin da ke kaina iyakacin iyawata a kuma dukkan sassan kasar nan.

"A yanzu da jama'a suka gane laifinsu da kuskurensu, zan iya addu'ar Allah ya yafe mana baki daya," tace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, ministan ta kai ziyara ga Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, inda sarkin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duban lamarin tsaron jihar.

"Gwamnatin tarayya ta taimaka ta bada tallafi ga jihar nan ta hanyar samar da tituna da za su fallasa 'yan ta'addan tare da bai wa jami'an tsaro damar yakarsu.

"A kuma dubemu ta fuskar nade-naden gwamnatin tarayya saboda a halin yanzu babban sakataren tarayya daya garemu.

"Ina tabbatar da cewa za mu cigaba da goyon bayan duk wasu shirye-shiryen gwamnatin tarayya wanda aka yi domin inganta rayuwar jama'a," Sarkin yace.

KU KARANTA: Gwamnan Osun ya bai wa masu satar kayan tallafi wa'adi, ya sanar da abinda za su iya fuskanta

Minista Sadiya Farouk ta yi martani bayan 'yan Najeriya sun bukaci ta yafe musu
Minista Sadiya Farouk ta yi martani bayan 'yan Najeriya sun bukaci ta yafe musu. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: UGC

KU KARANTA: Harbin Lekki: Buhari ya magantu, ya aike muhimmin sako ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, mazauna jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya sun fasa ma'adanar kayan tallafin COVID-19 da aka bai wa jihar. Kamar kowacce jihar, sun kwashi iyakar kayan da za su iya kwasa sannan suka yi awon gaba da su, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Balle wuraren adana tallafin korona a jihohi ya fara daga yankin kudancin kasar nan bayan zanga-zangar EndSARS. Lamarin ya cigaba da shigowa jihohin arewa inda fusatattun matasa ke nemo ma'adanar kayan rage radadin.

Sakamakon yawaita balle ma'adanar kayayyakin tallafin, gwamnatocin jihohi daban-daban sun saka dokar ta-baci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel