Bidiyo: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai

Bidiyo: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai

- An kama wani mutum da ake zargin ya saci wayar salular ma'aikaciyar jinyar da ke kula da shi a asibiti

- A cikin bidiyon da aka wallafa, ma'aikacin asibitin ya yi iƙirarin cewa an yi wa matashin magani kyauta amma ya sace wayar ya saka cikin ɗan kamfansa

- Ma'aikacin asibitin ya ce har kuɗin motar da za ta kai mutumin gida an biya masa kyauta amma ya saka musu da sharri

Ana zargin wani mutum da aka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa rai a hannun Allah a ranar 20 ga watan Oktoba da sata.

Ana kyautata zaton yana daga cikin matasan da suka jikkata ne yayin zanga zangar EndSARS da aka yi a Legas.

Bidiyo: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai
Bidiyo: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai. Hoto dada @lindaikeji
Asali: Instagram

An kai mutumin wani asibitin kudi don masa magani kuma ya kwashe kwanaki ana masa magani kyauta a Asibitin.

DUBA WANNAN: Kai ne sanadin matsalar mu: Fusattun matasa sun ƙona mutum-mutumin marigayi Nnamdi Azikwe (Hotuna)

A cikin bidiyon da aka wallafa, wani ma'aikacin asibitin ya yi zargin cewa mutumin ya sace wayar salular ɗaya daga cikin ma'aikatar jinyar da ke kula da shi.

A cewarsa, mutumin ya ɓoye wayar salular a cikin ɗan kamfansa.

KU KARANTA: Da duminsa: Matasa sun ƙona gidan sanata a Nigeria (Bidiyo)

Ga dai bidiyon a ƙasa.

A wani labarin daban, an ruwaito cewa mutum biyar sun rasu yayin da suka ƙoƙarin rabon wani adadin kudi da suka tsinta a maj'ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen sun ɓalle wurin ajiyar abincin ne inda suka tsinta jakuna biyu ɗauke da kuɗi ƴab dubu-dubu kusa da sakatariyar Kungiyar Kirista ta Najeriya a Jalingo ranar Asabar.

Daga nan ne suka yi watsi da abincin suka fara kokowar yadda za su raba kuɗin da suka tsinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel