Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara

Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara

- Rundunar dakarun soji na Operation Safe Haven ta damke wasu mutum 30 a ranar Lahadi

- Ana zargin matasan 30 da shiga gidan Yakubu Dogara tare da washe shi tas a Jos

- Maza 13 da mata 17 an kama su a Jos dauke da wasu kayayyaki na gidan tsohon kakakin majalisar

Rundunar Operation Safe Haven (OPSH) da ke kula da tsaro a jihar Filato ta cafke 'yan daba 30 da ake zargi da hannu cikin hari tare da sace kayayyakin gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a ranar Lahadi.

Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara
Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Wadanda ake zargin sun hada da maza 13 da mata 17 wadanda sojoji suka tare da adana su a hedkwatarsu da ke Jos karkashin shugabancin kwamandansu, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo.

Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara
Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wawushe tallafin Covid-19: Mutum 11 sun rasa rayukansu

'Yan daban da tarin yawansu sun shiga gidan Dogara da ke Lamingo kusa da asibitin koyarwa na jami'ar Jos wurin karfe 10 na safe a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba. Sun kai wa dan uwansa hari kafin su kwashe kayayyakin gidan.

Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara
Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Wata majiya da ke da kusanci da gidan ta ce wasu jama'a da ke da makwabtaka da gidan duk an ci zarafinsu sannan an kwashe musu kayayyaki, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne

Abubuwan da aka samu daga wurinsu sun hada da injin markade 5, kan injin markade 3, adaidaita sahu biyu da ba a bada ba, injin adaidaita sahu 1 da kuma sutturu da ba a dinka ba.

Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara
Hotunan matasa 30 da aka kama bayan yashe gidan Yakubu Dogara. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

A wani labari na daban, a ranar Lahadi, wasu bata-gari sun shiga tare da yashe gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ke kusa da asibitin koyarwa na jami'ar jihar Filato.

Jaridar Punch ta gano cewa, 'yan daban sun take dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka musu inda suke ta kusatwa gine-gine domin neman kayan tallafin korona.

An kai harin gidan Dogara da karfe 9 na safe, wata majiya da ta kasance ganau ba jiyau ba ta sanar da Jaridar Punch.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel