Yanzu haka: Ana musayar wuta tsakanin mayakan ISWAP da sojoji a Borno

Yanzu haka: Ana musayar wuta tsakanin mayakan ISWAP da sojoji a Borno

- Kamar yadda labarai daga majiya mai karfi ta sanar, ana musayar wuta tsakanin 'yan ISWAP da sojojin Najeriya

- Hakan na faruwa ne wurare biyu mabanbanta amma a lokaci daya a jihar Borno da ke arewa maso gabas

- Majiyar ta sanar da jaridar HumAngle cewa lamarin na faru ne a yanzu da yammacin ranar Lahadi

Mayakan ta'addanci na ISWAP, wadanda wani bangare ne na Boko Haram a halin yanzu suna musayar ruwan wuta tsakaninsu da dakarun sojin Najeriya.

Hakan yana faruwa ne a wurare biyu mabanbanta da ke Tungushe kusa da Monguno da kuma karamar hukumar Damboa.

Kamar yadda majiya wacce ganau ce ba jiyau ba ta sanar da jaridar HumAngle, hakan yana faruwa ne a yammacin ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2020.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel