Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne

- Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da halaka wasu mutum 6 da take zargi da zama 'yan Boko Haram

- Kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim ya ce mayakan sun kai hari a ranar Asabar har garin Babbangida inda suka yi barna

- Ya ce jami'in dan sanda daya ya rasu yayin da wani ya samu raunika bayan mausayar ruwan wutan da aka yi

Rundunar 'yan sandan jihar Yobe a ranar Lahadi ta ce jami'anta sun yi nasarar halaka mutum 6 da ake zargi da zama mayakan ta'addanci na Boko Haram, saboda harin da suka kai garin Babban gida da ke karamar hukumar Tarmuwa ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Dungus Abdulkarim, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Damaturu.

Abdulkarim ya ce jami'an 'yan sandan sun harbe shida daga cikin wadanda ake zargin, jaridar vanguard ta wallafa.

"Zakakuran jami'anmu sun dage inda suka yi musayar wuta da 'yan ta'adda inda suka kashe 6 kuma sauran suka tsere da miyagun raunika.

"'Yan ta'addan sun kona wata motar sintiri, sun lalata wani sashi na sakateriyar karamar hukumar, ofishin 'yan sanda da kuma wani wurin sojoji kafin a fatattakesu," yace.

Ya ce wani dan sanda ya rasu sannan wani ya samu miyagun raunika sakamakon musayar wutar da aka yi tsakaninsu da 'yan ta'addan, jaridar Vanguar ta wallafa.

Kamfanin Dillancin Labaran ya ruwaito cewa, harin da aka kai garin Babangida an kai shi ne a ranar Asabar, hakan ya janyo barna ga kadarorin gwamnati tare da tsorata mazauna yankin.

KU KARANTA: Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun damke mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne
Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun damke mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasar Najerya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nuna damuwarsa a kan harbe-harbe da kashe-kashen 'yan Najeriya da aka yi sakamakon bukatar kawo karshen cin zarafin 'yan sanda da suka yi a kasar nan.

Ya bayyana hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, The Punch ta tabbatar.

Mataimakin shugaban kasar wanda yace ya samu zantawa da wasu wadanda aka kwantar a asbitoci, ya ce wadanda aka harba ko aka kashe sakamakon zanga-zangar za a tabbatar da an bi musu hakkinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel