Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda

Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda

- Idan ba'a manta ba, ranar 21 ga watan Oktoba 2020 ne Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya dakatar da duk wani jami'in dan sanda daga kula da lafiyar masu fadi aji

- Sifeta janar ya ce banda jami'an gidajen gwamnati, masu kula da lafiyar Shugaban majalisar Dattawa da kuma na kakakin majalisar wakilai

- Amma duk da hakan, akwai Sanatoci, manyan 'yan kasuwa da kuma manyan 'yan siyasa da har yanzu suka cigaba da yawo da 'yan sanda kamar da

Akwai alamu har yanzu akwai wasu 'yan siyasa, manyan 'yan kasuwa da manyan mutane da 'yan sanda ke tsaron lafiyarsu.

Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya bayar da wani umarni a ranar 21 ga watan Oktoba, 2020, ga duk kwamishinonin 'yan sanda, inda yace lallai su dakatar da duk jami'ansu masu tsaron lafiyar 'yan siyasa, manyan 'yan kasuwa da kuma Wasu masu fadi aji.

Adamu bai hada da 'yan sanda masu kula da gidajen gwamnati da masu kula da lafiyar Shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ba.

Kamar yadda ya sanar, "Sifeta Janar na 'yan sanda ya umarceku da ku dakatar da kula da Lafiyar duk wasu masu fadi a ji banda gidajen gwamnati, Shugaban majalisar dattawa da na kakakin majalisar wakilai take-yanke.

"Duk wani jami'in da aka kama ya cigaba da raka ko kuma gadin wani babban mutum wanda kwamandansa ne ya umarcesa da yin hakan, to za'a kori kwamandan."

Bayan bayar da wannan umarnin da kwanaki 3, ranar Lahadi, jaridar PUNCH ta bayyana wasu Sanatoci, 'yan majalisar wakilai, manyan 'yan kasuwa da kuma manyan 'yan siyasa wadanda aka dakatar daga ajiye jami'an 'yan sanda masu kula da lafiyarsu, sun cigaba da hakan.

Wasu sanatoci da suka cigaba da yawo da masu kula da lafiyarsu sun sanar da wakilin PUNCH cewa sun daidaita da Sifeta janar din.

Wani jami'i mai kula da lafiyar wani sanata ya sanar da wakilin PUNCH cewa umarnin Sifeta janar bai shafesa ba.

Wani sanata cewa yayi, "Mu jami'an gwamnati ne, wadanda a kowanne lokaci za'a iya kai mana hari, idan muka cigaba da yawo babu jami'an tsaro ai akwai matsala."

KU KARANTA: Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi

Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda
Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda. Hoto daga @DailyNigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta

A wani labari na daban, zanga-zangar EndSARS ta canja salo cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar The Nation ta wallafa.

A jawabin da shugaban kasa yayi da daren Alhamis, wanda ya ja kunnen wadanda suka yi uwa da makarbiya a kan zanga-zangar ya ce lallai gwamnatin tarayya ba za ta yarda da sauran ta'addanci ba.

Yace: "Wajibi ne in ja kunnen wadanda suka canja wa zanga-zangar EndSARS salo daga asalin makasudinta, wadda matasa suka fara a kan dakatar da rundunar SARS."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel