Mun damke mutane 229 cikin wadanda sukayi sace-sace da kone-kone a Legas - Sanwo-Olu
- Kwana biyu bayan bannar da aka yi, hukuma ta fara aikinta
- Ministan Shari'ar Legas ya shirya gurfanar da wadanda ake zargi da laifi kotu
- Jihar Legas ta yi asarar dukiya na sama naira tiriliyan daya cikin kwanaki biyun da suka gabata
Ma'aikatar Shari'ar jihar Legas za ta hukunta mutane 229 da yan sanda suka damke da zargin amfani da zanga-zangan EndSARS wajen lalaci, da fashin dukiyoyin gwamnati da na mutane masu zaman kansu.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta samu jawabin daga Diraktan labaran ma'aikatar, Mr Kayode Oyekanmi.
Jawabin yace diraktar hukunta mutane a jihar, Mrs Olayinka Adeyemi, ta tanadi yan sanda na musamman don hakan.
A cewar jawabin, hukuma ta tara lauyoyi wajen duba wadanda aka kama dumu-dumu domin sanin yadda za'a bi da lamarinsu.
Kawo yanzu, an damke mutane 229 kan laifuka daban-daban wanda ya hada da kone-kone, kisan kai, sata, lalata dukiya da kuma saba dokar hana fita.
DUBA NAN: Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA

Asali: Twitter
KU KARANTA: Matasa sun kai farmaki dakin ajiyan kayan talafin Korona, sun debi buhuhunan hatsi
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu a ranar 20 ga Oktoba ya sanya dokar hana fita domin kwantar da tarzoman da ya fara tashi a jihar.
"Ma'aikatar Shari'ar jihar Legas ta ce bayan tsare-tsare za'a gurfanar da wanda aka tabbatar na da laifi gaban kotu kuma a saki maras laifi," cewar jawabin
NAN ta ruwaito cewa wasu bata gari sun mamaye filin zanga-zangan da matasa ke yi na bukatar kawo karshen yan sandan EndSARS saboda cin zarafin da sukeyi.
Ga jerin wuraren da aka kaiwa hari:
1. Hukumar kula da tashan jirgin ruwa - An banka wuta
2. Ofishin yan sandan Orile - An banka wuta
3. Garajin Lekki - An banka wuta
4. Tashar Motar BRT dake Oyingbo - An bankawa sabbin motoci wuta
5. Gidan talabijin TVC, Ketu Legas - An banka wuta
6. Ofishin VIO, Ofishin FRSC, Ojodu - An banka wuta
7. Tashar wutan BRT, Ojodu Legas - An banka wuta
8. Tashar BRT dake Berger - An banka wuta
9. Gidan talabijin jihar Legas,Agidingbi, Ikeja - An banka wuta
10. Wajen shakatawa, Oregun, Legas - Agidingbi, Ikeja
11. Fadar Sarkin Legas - An banka wuta
12. Gidan mahaifiyar gwamnan Legas Surulere Legas - An banka wuta
13 Makarantar Kings College
14. Oriental Hotel, Victoria Island Lagos
KU KARANTA: Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a
15. Sassan bankin AccessBank - An banka wuta
16. Sassan bankin GTBank - An banka wuta
17. Sakatariyan karamar hukumar Ajeromi
18. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Island
19. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Island East
20. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Mainland
21. Sakatariya Ibeju Lekki LCDA
22. Gidan babban yayan gwamnan Legas dake Lagos Island
23. Gidan jaridar The Nation
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng