An sace ma'aikacin jami'ar FUD a hanyarsa ta zuwa Kano

An sace ma'aikacin jami'ar FUD a hanyarsa ta zuwa Kano

- Masu garkuwa da mutane sun sace wani ma'aikacin jami'ar tarayya ta Dutse na jihar Jigawa

- An yi garkuwa da Shehu Abdulhamid ne a ranar Juma'a 23 ga watan Oktoba a hanyarsa ta zuwa Kano

- Masu garkuwa sun tafi da shi daji amma suka ƙyalle abokin tafiyarsa ta tafi gida ya faɗa abinda ya faru

An sace ma'aikacin jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse (FUD), jihar Jigawa mai suna Shehu Abdulhamid a jihar Kano kamar yadda LIB ta ruwaito.

Mai magana da yawun jami'ar, Abdullahi Bello ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a 23 ga watan Oktoban shekarar 2020.

An sace ma'aikacin jami'ar FUD a Kano
An sace ma'aikacin jami'ar FUD a Kano. Hoto daga Lindaikeji.com
Asali: Twitter

Ya ce an sace Abdulhamid ne a ranar Alhamis a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Matasa sun ƙona gidan sanata a Nigeria (Bidiyo)

Abdulhamid, wadda ke aiki a asibitin jami'ar yana hanyar sa ta zuwa Kano daga Jigawa ne tare da abokinsa a motarsa a lokacin da aka sace shi aka shiga da shi daji a Gaya.

"Masu garkuwa sun bukaci abokin tafiyarsa ya tafi da motar ya tafi ya faɗa wa iyalansa abinda ya faru," in ji Bello.

"Sun fara tattaunawa. Masu garkuwa sun nemi naira miliyan 20 amma zuwa ranar Asabar suna neman Naira miliyan 1.5," ya ƙara cewa.

KU KARANTA: Yaɗa kalaman ƙiyayya: Majalisar Ƙolin Musulunci da CAN sun mayar wa hadimin Buhari martani

Mai magana da yawun jami'ar ya kuma ce an sanar da rundunar yan sanda a Jigawa.

Amma Kakakin yan sanda na jihar Jigawa Audu Jinjiri ya ce a a Jigawa abin ya faru ba don haka sun sanar da rundunar ƴan sandan Kano.

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita a wasu unguwanni a ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun.

A cewar sanarwar garuruwan da abin ya shafa sun a Kaduna ta Kudu sun hada da Barnawa, Kakuri da Television. Gwamnan Kaduna Nasir El Rufai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel