Da ɗumi-ɗumi: An saka dokar hana fita a fadin jihar Kaduna

Da ɗumi-ɗumi: An saka dokar hana fita a fadin jihar Kaduna

- Gwamna Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita a dukkan ƙananan hukumomi jihar Kaduna

- Da farko dokar ta shafi Ƙananan hukumomin biyu ne da suka hada da karamar hukumar Kaduna ta Kudu da Chikun

- Gwamnan ya saka dokar ne biyo bayan afkawa wasu ma'aijiyar kayan abinci da aka yi a ranar Asabar

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita a dukkan ƙananan hukumomin da ke jihar Kaduna.

Tunda farko, gwamnan ya sanar da saka dokar hana fitar ne a kananan hukumomi biyu wata Kaduna ta Kudu da kuma Chikun.

Amma daga bisani ya kara fadada dokar zuwa dukkan kanananan hukumomin jihar inda ya ce an yi hakan ne don kiyayye lafiyar al'umma da dukiyoyinsu.

Da ɗumi-ɗumi: An saka dokar hana fita a jihar Kaduna
Gwamnan Kaduna Nasir El Rufai. Hoto daga Dailytrust.ng
Asali: Twitter

.

DUBA WANNAN: Yaɗa kalaman ƙiyayya: Majalisar Ƙolin Musulunci da CAN sun mayar wa hadimin Buhari martani

Gwamnan ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar 24 ga watan Oktoban 2020.

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnan ya saka dokar ne bayan kutse da wasu mutane suka yi a ma'ajiyar abinci da ake zargi na korona ne a ƙananan hukumomin biyu.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Iwo a Osun

Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ta ce an bawa jami'an tsaro umurnin kama duk wanda aka samu ya saba dokar hana fitan.

"An umurci jami'an tsaro su kama duk wanda aka samu yana fashi ko lalata kayayyaki a kuma gurfanar da shi gaban kotu," a cewar sanarwar.

Ya kuma yi kira da mazauna jihar su rungumi zaman lafiya su guji duk wani abu da ka iya tada hankali ko rushewar doka da oda.

A wani labarin, wasu da ake zargi ƴan daba ne a ranar Asabar sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin dan jamiyyar APC mai wakiltar Oyo Central da ke Ibadan sun sace kayan tallafi da kuɗin su ya kai N200m.

Folarin ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin yayin wani shirin gidan rediyo a ranar Asabar a Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel