An sace babura 300 da wasu kayayyaki a gidan sanata a Ibadan

An sace babura 300 da wasu kayayyaki a gidan sanata a Ibadan

- Wasu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin a Ibadan

- Matasan sun sace kayayyaki kamar babura da firinji da kuɗin su ya kai naira miliyan 200

- Sanata Folarin ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce kayan tallafi ne da zai raba a watan Disamba

Wasu da ake zargi ƴan daba ne a ranar Asabar sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin dan jamiyyar APC mai wakiltar Oyo Central da ke Ibadan sun sace kayan tallafi da kuɗin su ya kai N200m.

Folarin ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin yayin wani shirin gidan rediyo a ranar Asabar a Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An gano cewa kayayyakin da aka sace na tallafi ne ga mazabarsa da ɗan majalisar zai yi a watan Disamba.

An sace babura 300 da wasu kayayyaki a gidan sanata a Ibadan
Sanata Folarin Teslim. Hoto daga Dailytrust.ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yaɗa kalaman ƙiyayya: Majalisar Ƙolin Musulunci da CAN sun mayar wa hadimin Buhari martani

Cikin kayayyakin akwai babura 300, firinji masu ƙanƙara da kayan abinci.

Folarin, tsohon shugaban kwamitin samar da kayan cikin gida kuma tsohon jagora a majalisar dattawa ya ce hankalinsa ya kwanta tunda ba a rasa rai ba.

Wasu mazauna yankin sun yi Allah wadai da lamarin inda suka ce akwai banbanci tsakanin zanga-zanga da fashi.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Iwo a Osun

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce lamarin yana wuce gona da iri ya kuma yi kira ga ƴan daban su dena aikata munannan ayyuka.

A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan daba sun ne sun kai hari gidan iyayen Sanata Gershom Bassey da ke wakiltan Calabar South a ranar Asabar 24 ga watan Oktoba.

'Yan daban sun sace kayayyaki daga gidan da ke Calabar, babban birnin jihar kana daga bisani suka cinna wa gidan wuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel