Da duminsa: Matasa sun ƙona gidan sanata a Nigeria (Bidiyo)

Da duminsa: Matasa sun ƙona gidan sanata a Nigeria (Bidiyo)

- Ana ci gaba da kai hare hare kan gidajen manyan 'yan siyasa duk da dokar ta baci da aka saka a wasu jihohi

- Wasu matasa sun yi kutse cikin gidan Sanata Gershom Bassey da ke birnin Calabar a jihar Cross Rivers

- Matasan da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun yi wa jami'an tsaro karfa-karfa sannan suka samu ikon shiga gidan

Wasu da ake zargin 'yan daba sun ne sun kai hari gidan iyayen Sanata Gershom Bassey da ke wakiltan Calabar South a ranar Asabar 24 ga watan Oktoba.

'Yan daban sun sace kayayyaki daga gidan da ke Calabar, babban birnin jihar kana daga bisani suka cinna wa gidan wuta.

Da duminsa: Matasa sun ƙona gidan sanata a Nigeria (Bidiyo)
Da duminsa: Matasa sun kwashe kaya sun ƙona gidan sanata a Nigeria (Bidiyo). Hoto daga Vanguard NGR
Asali: Twitter

Bidiyon yadda abin ya faru dake yawo a yanar gizo, ya nuna wasu matasa sun dauki katifa, talabijin, kujeru da kuma tukunyar gas daga gidan.

DUBAW WANNAN: Kai ne sanadin matsalar mu: Fusattun matasa sun ƙona mutum-mutumin marigayi Nnamdi Azikwe

News Wire NGR ta ruwaito cewa maharan sunyi wa jami'an tsaron dake tsaron gidan karfa- karfa kafin su sami damar shiga ginin.

Wasu yan ta'adda kuma, sun shiga gidan tsohon shugaban majalisar dattawa, Victor Ndoma Egba a Calabar suka kuma yi awon gaba da wasu kayayyakin amfanin gida, suka kuma lalata motoci.

KU KARANTA: Yaɗa kalaman ƙiyayya: Majalisar Ƙolin Musulunci da CAN sun mayar wa hadimin Buhari martani

Gidajen manyan yan siyasa irin su Ndoma Egba da Liyel Imoke suna ci gaba da fuskantar hare hare duk da dokar ta baci da aka saka a jihar.

Ndoma Egba ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Nuwambar 2015.

Shine mataimakin shugaban majalisa ta 6 (2007- 2011) kuma shugaban majalisar (2011 - 2015). An nada shi a matsayin shugaban hukumar ci gaban Niger Delta (NDDC) a Yuli 2016.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164