El-Zakzaky yana nan da ransa - IMN

El-Zakzaky yana nan da ransa - IMN

- Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da Shi'a ta karyata labarin cewa shugaban ta Ibrahim Zakzaky ya mutu

- Wani mamba a kungiyar mai suna Abdullahi Usman ya tabbatar da cewa shugaban su yana nan da ransa

- Jita-jitar rasuwar Zakzaky ya bazu a garin Kaduna inda ya jefa tsoro zukatan mutane har wasu sun takaita zirga-zirga

Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Shiekh Ibrahim El-Zakzaky yana nan da ransa kamar yadda wani dan kungiyar mai suna Abdullahi Usman ya tabbatar.

El-Zakzaky yana nan da ransa - IMN
Ibrahim El-Zakzaky. Hoto daga Guardian.ng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun afka wurin da aka ajiye kayan tallafin korona a Osun

Daily Trust ta ruwaito cewa akwai jita-jita da ke yawo na cewa shugaban kungiyar da IMN da ake yi wa lakabi da Shi'a ya mutu.

Amma Usman yayin hira da majiyar Legit.ng ta yi da shi ta wayar tarho ya tabbatar da cewa Zakzaky yana nan bai mutu ba.

KU KARANTA: Kai ne sanadin matsalar mu: Fusattun matasa sun ƙona mutum-mutumin marigayi Nnamdi Azikwe

"Ban san daga inda mutane suka jiyo wannan jita-jitar ba, amma ina tabbatar maka cewa shugaban mu yana nan da ransa. Ba zai haifar wa gwamnati da mai ido ba idan shugaban mu ya mutu a hannun ta," ya kara da cewa.

Daily Trust ta ruwaito cewa labarin rasuwar Zakzaky ya jefa mutane cikin halin dar-dar a Kaduna inda wasu suka takaita zirga zirga don tsoron hari.

A wani labarin, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da aka saka a jihar a lokacin da rikici ya yi kamari a jihar sakamakon zanga zangar EndSARS.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Juma'a.

Da ya ke jawabi bayan ya ziyarci wuraren da aka yi rikici a jihar, gwamnan ya ce daga ranar Asabar mutane suna iya fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe shida na yamma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel