Da duminsa: 'Yan daba sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Iwo a Osun
- Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun afka sakatariyar karamar hukumar Iwo a jihar Osun
- Matasan sun cinna wa motocci da dama wuta sun kuma shiga ofisoshi sun sace kayayyaki tare da lalata wasu
- Wani jami'in gwamnati a jihar a tabbatar da afkuwar lamarin amma ya bukaci a sakayya sunansa
'Yan daba a ranar Asabar sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Iwo ta Kudu a jihar Osun da ke Kudu maso yammacin Najeriya.
Yayin harin, 'yan daban sun lalata kayayyaki sannan sun cinnawa motocci wuta, kamar yadda majiya daga fadar Oluwo na Iwo suka tabbatar.
![Da duminsa: 'Yan daba sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Iwo a Osun Da duminsa: 'Yan daba sun kai hari sakatariyar karamar hukumar Iwo a Osun](https://cdn.legit.ng/images/1120/59a87511902d852b.jpeg?v=1)
Asali: UGC
DUBA WANNAN: Rayuka 69 suka salwanta sakamakon zanga zanga EndSARS, inji Buhari
Wasu da abin ya faru a idonsu sun shaidawa The Punch cewa 'yan daban sun kuma sace kayayyaki daga ofisoshin da ke sakatariyar.
Daya daga cikin mambobin majalisar da ya nemi a sakayya sunansa shima ya tabbatar da harin.
'Yan daban da suka fito da yawa sun kuma kutsa cikin wani gidan gona mai suna Tuns Farm da ke kan titin Osogbo/Ikirun sun sace kayayyaki.
KU KARANTA: Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya (Bidiyo)
Wani hadimin shugaban karamar hukumar Iwo ta Kudu, wanda shima ya nemi a sakayya sunansa ya tabbatar cewa wasu 'yan daba sun kai hari a sakatariyar karamar hukumar ta Iwo.
A wani labarin, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da aka saka a jihar a lokacin da rikici ya yi kamari a jihar sakamakon zanga zangar EndSARS.
Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Juma'a.
Da ya ke jawabi bayan ya ziyarci wuraren da aka yi rikici a jihar, gwamnan ya ce daga ranar Asabar mutane suna iya fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe shida na yamma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng