Bayan zanga-zangan kwanaki 13, mutane 77 kacal suka kamu da Korona ranar Juma'a

Bayan zanga-zangan kwanaki 13, mutane 77 kacal suka kamu da Korona ranar Juma'a

- Hukumar NCDC ta daina sakin adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar Korona a shafukanta na Facebook da Tuwita

- Yanzu duk mai bukatar gani sai ya garzaya shafin hukumar

Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 77 ranar Juma'a a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 61,882 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Juma'a, 23 ga watan Oktoba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane kimanin 62,000 da suka kamu, an sallami 57,190 yayinda 1129 suka rigamu gidan gaskiya.

A cewar NCDC, mutane 3,662 ke jinya yanzu.

Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu– Lagos (11), Kaduna (20), Rivers (19), FCT (4), Osun (3), Ondo (2), Sokoto (2), Kwara (2), Benue (2), Imo (1), Ogun (1)

DUBA NAN: Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona - Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami'an tsaro

Bayan zanga-zangan kwanaki 13, mutane 77 kacal suka kamu da Korona ranar Juma'a
Bayan zanga-zangan kwanaki 13, mutane 77 kacal suka kamu da Korona ranar Juma'a Hoto: NCDC
Asali: UGC

KU KARANTA: Matasa a jihar Cross River sun debi tallafin Korona a ma'ajiya (Bidiyoyi)

Kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, ta shiga jerin masu kira ga matasa masu zanga-zangar #ENDSARS su sassauta kuma su amince da sulhu saboda har yanzu akwai cutar Korona a gari.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a hira da manema labarai a Abuja, The Sun ta nakalto

Mustafa ya siffanta masu zanga-zangan a matsayin manyan masu iya yada cutar kuma za'a fara ganin sakamakon hakan nan da makonni biyu masu zuwa.

"Maganar gaskiya shine, nan da mako biyu masu zuwa, idan ka tattara dukkan masu taro a Lekki Toll Plaza, za ka samu masu cutar da dama, " Mustafa yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel