Yaɗa kalaman ƙiyayya: Majalisar Ƙolin Musulunci da CAN sun mayar wa hadimin Buhari martani

Yaɗa kalaman ƙiyayya: Majalisar Ƙolin Musulunci da CAN sun mayar wa hadimin Buhari martani

- Kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, da Majalisar Kolin Musulunci, NSCIA, sun mayar wa fadar shugaban ƙasa martani

- Kakakin Shugaban Femi Adesina ya yi iƙirarin cewa malaman addinai sun mayar da wuraren bauta kafar watsa sakonnin ƙiyayya wadda hakan na da alaƙa da EndSARs

- Addinan biyu sun yi wa fadar shugaban kasar kaca-kaca inda suka nesanta kansu da yaɗa kalaman ƙiyasta

Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya da Kwamitin ƙoli na harkokin addinin musulunci sun caccaki fadar shugaban ƙasa kan dora musu laifin haifar da zanga zangar EndSARS kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hadimin shugaban kasa Femi Adesina cikin wani rubutu da ya wallafa ya ce sakonnin ƙiyayya da ke fitowa da masallatai da coci suna da alaƙa da zanga zangar.

EndSARS: Majalisar Koli na musulunci da CAN sun caccaki hadimin Buhari
Femi Adesina. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: Babu tausasawa a kalaman Buhari - Marasa rijaye a majalisa

CAN da NSCIA, a mabanbantan hira da suka yi sun caccaki fadar shugaban kasar kan abinda suka kira dora laifi kan wasu a maimakon magance matsalar da ta taso.

A rubutun da Adesina ya wallafa mai taken, 'Idan Najeriya ta mutu, ƙiyayya ce ta kashe ta,' ya ce zanga zangar EndSARS dama ce ta yaɗa sakonnin ƙiyayya da masallatai da coci ke da hannu ciki.

A martanin ta, CAN, ta bakin Fasto Bayo Oladeji, mashawarcin shugaban ƙasa, Supo Ayokunle ta ce coci bane kuma a kullum za ta rika neman ganin inganta rayuwar al'umma.

KU KARANTA: Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya (Bidiyo)

Wani sashi cikin martanin Oladeji, "Yana da wahala a gano ko Femi Adesina yana fadin son ransa ne ko abinda ke zuciyar mai gidansa. Matsalar wasu hadiman gwamnati na samo asali ne da zarar sun fara tunanin sun fi kowa son Najeriya. Wannan abin takaici ne kuma ba daidai bane."

A bangaren ta, Kakakin NSCIA, Ibrahim Aselemi, ya ce, "NSCIA ta yi aiki sosai don wayar da kan shugabannin masallatai a Najeriya game da sharrin da ke tattare da kalaman ƙiyayya.

"A lokuta da dama, Majalisar ta kan nemi gwamnatin tarayya ta hukunta wasu da ke yaɗa kalaman ƙiyayya. Majalisar ta gargadi limamai da dama cewa wannan ba shine ƴancin faɗin ra'ayi ba. Don haka ban san inda Kakakin Shugaban Ƙasa ya samo wannan bayanin ba."

A wani rahoton daban, ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello a ranar Laraba ya kira taron tsaro na gaggawa a kan zanga zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ministan a jawabinsa na bude taro ya ce an kira taron ne, "Don bita kan abubuwan firgici da suka faru cikin mako daya da ya gabata" da nufin tabbatar da ganin lamura sun koma yadda suke a baya a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel