Kai ne sanadin matsalar mu: Fusattun matasa sun ƙona mutum-mutumin marigayi Nnamdi Azikwe (Hotuna)

Kai ne sanadin matsalar mu: Fusattun matasa sun ƙona mutum-mutumin marigayi Nnamdi Azikwe (Hotuna)

- Wasu fusatattun matasa sun huce fushin su a kan mutum-mutumin marigayi Dakta Nnamdi Azikwe a Onitsha

- A cewar rahoton, matasan yayin da suke cinna wa mutum-mutumin wuta sun zargi Azikwe da zama sillar matsalolin da Najeriya ke fuskanta

- Azikwe shine mutum na farko da ya zama shugaban kasar Najeriya daga shekarar 1963 zuwa 1966

Mutum mutumin tsohon shugaban Najeriya, marigayi Dakta Nnamdi Azikwe, yasha wuta a hannun 'yan tawayen da ke fakewa da zanga zangar #ENDSARS a Onitsha, jahar Anambra.

Gunkin yana kana iya shataletalen makarantar Dennis memorial grammar school, Unguwar Akwa, Onitsha da aka fi sani da shataletalen Zik kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lokacin da suke aikata barnar, an jiyo masu zanga zangar suna ihun cewa, "kai ka janyo mana wannan masifar da ka hade Najeriya a matsayin kasa daya", "kai ka janyo mana wannan wahalar", dama wasu munanan kalaman.

Shi ya jefa mu cikin halin da muka shiga: Masu zanga zanga sun rushe mutum mutumin Zik
Matasa sun kona mutum mutumin Nnamdi Azikiwe a Anambra. Hoto daga PM News
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun afka wurin da aka ajiye kayan tallafin korona a Osun

Da yake bayyana lamarin, wani zuri'ar Azikwe, Victor Ononye, ya bayyana al'amarin a matsayin abun tsoro da fargaba.

Yace, "dole duk inda ran shugaban Najeriyar na farko Dr. Nnamdi Azikwe yake, to dole yana cike da nadamar karbarwa Najeriya yanci.

"Abun da ya faru a shataletalen DMGS, Onitsha, wanda na gani da idona ya sani zubar da hawaye.

"Wasu marasa da'a, yan ta'adda, yan bindiga dadi, shashai, marasa tunani, banzaye, dakikai kuma yan iska sun farfasa gunkin, suka kuma saka taya a wuyansa suka zuba fetur suka kuma cinna masa wuta.

Shi ya jefa mu cikin halin da muka shiga: Masu zanga zanga sun rushe mutum mutumin Zik
Fusatattun matasa sun kona mutum mutumin Nnamdi Azikwe. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Babu tausasawa a kalaman Buhari - Marasa rijaye a majalisa

"Sun balle sandar girman da ke hannunsa sun kuma tafi da ita. Wannan rashin tunani irin na jahilan da basu san tarihi ba.

"Sun lalata abubuwa da dama da aka yiwa gunkin ado dasu tare da yi musu caka-caka. Basu da wani yawa. Mai yasa yan sandan da suke yar tafiya kalilan daga shataletalen ba zasu iya tarwasu ba.

"Naga jami'an sintiri guda biyu sun zo a babur suna rike da bindiga. Suka tsaya yan bangar suka yi musu dadin baki suka tafi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164