EndSARS: Babu tausasawa a kalaman Buhari - Marasa rijaye a majalisa

EndSARS: Babu tausasawa a kalaman Buhari - Marasa rijaye a majalisa

- Bangaren marasa rinjaye na majalisar wakilan tarayya sun ce babu tausayi a tare da jawabin da Shugaba Buhari ya yi kan EndSARS

- 'Yan majalisan sun ce abinda suke tsammani shine jawabin na Buhari ya kunshi kalamai masu tausasa zuciya da kwantar da hankula

- 'Yan majalisar sunyi kira ga Shugaba Buhari ya gaggauta samar da zaman lafiya a kasar tare da hukunta wadanda ake zargi da kisa

Bangaren marasa rinjaye a majalisar tarayya tace bayan nazari ga kalaman Shugaba Buhari akan zanga zangar #ENDSARS, jawabin nasa bai gamsar da dama cikin 'yan Najeriya ba kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Marasa rinjayen sunce abun mamaki ganin yadda shugaban bai yi magana akan kisan da ake zargin an yi wa mutanen da ba suji ba basu gani ba a Lekki, lamarin daya haddasa fitintunu da dama a fadin kasar nan, wanda suka ce hakan yana bukatar shugaban ya yi magana akai.

Babu tausasawa a kalaman Buhari - Marasa rijaye a majalisa
Shugaba Buhari da Majalisar Wakilai na Tarayya. Hoto @MobilePunch/ Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun afka wurin da aka ajiye kayan tallafin korona a Osun

A wani jawabi da shugaban marasa rinjayen, Ndudi Elumelu ya yi yace suna saka ran jawabin shugaban ya ƙunshi, "Yazo da kalaman tausasawa ga wanda harbin Lekki ya shafa da kuma wasu zalunci da jami'an tsaro suka aikata, ya kamata ace kalaman nasa sun kunshi kalaman sanyaya zuciya."

An sawa kudirin sunan 'EndSars: Kalaman Buhari suna bukatar garambawul - Marasa rinjayen Majalisa'.

Wani sashi na jawabin ya ce, "A matsayinmu na wakilan al'umma, muna kira ga Shugaba Buhari a matsayin sa na uban kasa da ya dauki matakan gaggawa wajen dawo da zaman lafiya a fadin kasar nan ta hanyar hukunta wanda suka aikata laifukan kisa."

DUBA WANNAN: EndSARS: Adesina ya dora laifi kan masallatai da coci-coci

A daya bangaren masu rinjayen majalisar sun bukaci Buhari daya gaggauta sake fasalin tsaro "ta hanyar canja manyan hafsoshin tsaron kasar nan da wanda zasu kawo sauye sauye da dama don maganin ayyukan ta'addanci a kasar nan.

"Marasa rinjayen sunce an kafa mummunan tarihi, sun kuma bukaci da ya kamata a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin 'yan kasa."

"Sun kuma ce suna jajantawa iyalan wanda harin ya rutsa dasu, sun kuma bukaci da a tabbatar an dauki matakin da zai dawo da zaman lafiya don jin dadin kowane dan kasa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel