Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona - Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami'an tsaro

Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona - Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami'an tsaro

- Bayan samun labarin ana diban kayan tallafin Korona, gwamnan Cross RIver ya aika sako mai muhimmanci ga jami'an tsaro

- Mai magana da yawun gwamnan ya saki jawabi da yammacin Juma'a

- Gwamnan ya ce tuni ya fara raba kayan tallafin a yankunan karkara

Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya umurci jami'an tsaro kada su harbi kowa a inda matasa ke diban kayan tallafin Korona da gwamnatin ta boye, cewar rahoton Vanguard.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Mr Christian Ita, ya saki, ya ce gwamna Ben Ayade ya umurci jami'an tsaro da aka tura tabbatar da tsaro a wurare kada su harbi mutanen da suka balla gidan ajiyan abinci.

Ya ce gwamnatin ta ajiye kayan tallafin ne domin rabawa mutanen karkara.

"Makonni biyu da suka gabata aka kawo mana kayan abincin kuma mun fara rabawa musamman a karkara, " yace.

"Gwamnan ya ce akwai takaici wasu bata gari sun kwace zanga-zangar lumanan da matasa suka fara kan cin zarafin yan sanda,"

Ya yi kira ga kowa a jihar su cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya.

KU KARANTA: Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona - Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami'an tsaro
Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona - Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami'an tsaro credit: @OJay_Jahswill
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa wasu mutane a jihar Calabar sun afka dakin ajiya kayayyaki da ke Bishop Moynah Street, inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so.

Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a kai.

Gwamnatin jihar ta tara dubunnan kwalayen Indomie da ya kamata a rabawa mutane lokacin dokar kulle na Korona amma har yanzu ba'a raba ba.

DUBA NAN: Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina

Kalli bidiyon matasan suna diba:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel