Da duminsa: Matasa a jihar Cross River sun debi tallafin Korona a ma'ajiya (Bidiyoyi)

Da duminsa: Matasa a jihar Cross River sun debi tallafin Korona a ma'ajiya (Bidiyoyi)

- Maza da Mata a jihar Cross River sun gano dakin ajiyar kaya sun kwashi kayan abincin tallafin COVID-19

- Bidiyon ya nuna mutane maza da mata suna ta gaggawar shiga dakin ajiyar kayan abinci

- An kuma hasko wani dan sanda wanda ya baiwa wani nakasasshe rabonshi na gayan ganimar

Wasu mutane a jihar Calabar sun afka dakin ajiya kayayyaki da ke Bishop Moynah Street, inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so.

Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a kai.

Gwamnatin jihar ta tara dubunnan kwalayen Indomie da ya kamata a rabawa mutane lokacin dokar kulle na Korona amma har yanzu ba'a raba ba.

Wannan shine kusa jiha ta biyar da matasa zasu shiga dibar tallafin.

Kalli bidiyoyin:

KU KARANTA: Idan Najeriya ta tarwatse, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina

KU KARANTA: Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

Da duminsa: Matasa a jihar Cross River sun debi tallafin Korona a ma'ajiya (Bidiyoyi)
Da duminsa: Matasa a jihar Cross River sun debi tallafin Korona a ma'ajiya (Bidiyoyi) Credit: @OJay_Jahswill
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoto irin wannan da ya faru a jihar Kwara da yammacin nan inda matasa sun garzaya tashar jirgin Ilori inda aka ajiye kayan abincin tallafin Korona.

Wanda shin ya biyo bayan da wasu mutanen a jihar Osun suka yi kutse a wani dakin ajiye kaya a Ede suna kwashi kayan abincin zuwa gidajensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng