Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos

Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos

- Kamar yadda rikicin EndSARS ya barke a jihar Filato, kowa yana ta tunanin kafin al'amura su dawo kamar da za su iya daukar lokaci mai tsawo

- Amma abin ba haka bane, matasa sun yi ba-zata, inda suka kwantar da hankulansu kuma titunan sun koma fes tamkar babu abinda ya taba faruwa

- Yanzu haka, titin Ahmadu Bello kusa da titin Bauchi ya koma kamar da, hatta bankuna da wuraren shige da ficen kudade sun cigaba da harkokinsu

Rayuwa ta fara komawa daidai a kananan hukumomin Jos ta Arewa da kuma Jos ta kudu awanni kadan bayan sakakullen awanni 24 a kananan hukumomin guda biyu da ke jihar Filato.

A ranar Talata ne gwamna Simon Lalong yasa kullen awanni 24 bayan rikicewar garin sakamakon zanga-zangar EndSARS da ta koma tashin hankali a kan titin Ahmadu Bello.

Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos
Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

Kowa ya koma bakin sana'arsa a kasuwar Terminus da ke kan titin Ahmadu Bello, layin Bauchi, kuma tashar motar Bukuru ta koma kamar da.

Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos
Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari, sun sace matashi mai shekaru 24 a Abuja

Haka kuma bankuna da sauran wuraren shige da ficen kudi sun cigaba da aiwatar da ayyuka tamkar babu abinda ya faru, Daily Trust ta tabbatar.

Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos
Hotuna: Harkokin kasuwanci sun koma daidai bayan cire dokar kulle a Jos. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro tace Operation Lafiya Dole ta samu nasarar ragargazar 'yan Boko Haram 4, kuma ta kwace bindigogi AK47 a hannunsu, yayin da suka je aiki kauyen Sawa dake karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin, John Enenche, ya sanar da hakan yayin da yake bayar da bayani a kan ayyukan da rundunar suka yi a ranar Alhamis a Abuja.

A cewarsa, rundunar Operation Lafiya Dole ta sama da kasa sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'adda da dama da ke maboyarsu cikin sati daya a Arewa maso gabas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel