Alkali ya bukaci mahaifi ya yi wa diyarsa addu'a bayan ya maka ta a kotu

Alkali ya bukaci mahaifi ya yi wa diyarsa addu'a bayan ya maka ta a kotu

- Wata budurwa mai suna Ifeoma, mai shekaru 27 ta sawa mahaifinta guba a abinci, dama kuma ta taba karya masa kafa a 2007

- Mahaifinta, Samuel Madaukar, mai shekaru 65 ya kai kararta kotu, inda yace baya so a daure ta, yana so ne ta canja halayenta

- Ya kara da cewa, na jure cutarwarta na tsawon shekaru 15, yanzu haka ina da hawan jini, ina fatan ta canja rayuwarta

Wani Alkali dan Najeriya ya roki wani tsoho mai shekaru 65 ya yafe wa diyarsa kuma ya dinga yi mata addu'a.

Muhammad Adamu, wani alkalin kotu ne, wanda ya roki mahaifin wata Ifeoma mai shekaru 27, wadda aka kama da laifin cin zarafi, wulakanci da cutar da mahaifinta.

Kamar yadda bayanai suka zo, Ifeoma ta yi yunkurin sa wa mahaifinta, Samuel Maduakar guba a abinci.

Alkalin ya ce ya kamata Maduakar ya cigaba da yi wa Ifeoma addu'ar Allah ya canja ta, kuma ya amince da hakurin da ta bashi kuma ya yafe mata.

Alkalin ya yi wa Ifeoma nasiha, inda yace wajibi ne ta girmama mahaifinta saboda bata da kamarsa a duniya.

Wacce ake zargin ta yi dambe da mahaifinta inda ta ji masa raunuka, har ta taba karya masa kafa a 2007.

Mahaifin yace, "Ba na kawo kararta kotu don a daureta bane, Inaso ne ta dinga biyayya a gareni. Na jure miyagun halayenta na tsawon shekaru 15, kuma yanzu haka har hawan jini gare ni. Wadannan hawayen nata duk na yaudara ne, bana tunanin za ta canja."

KU KARANTA: EndSARS: Hukumar DSS ta magantu a kan zargin da ake mata, ta yi karin haske

Alkali ya bukaci mahaifi ya yi wa diyarsa addu'a bayan ya maka ta a kotu
Alkali ya bukaci mahaifi ya yi wa diyarsa addu'a bayan ya maka ta a kotu. Hoto daga Partners West Africa Nigeria
Asali: UGC

KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 4, sun samo manyan bindigogi 4 a Borno - DHQ

A wani labari na daban, Fatima Ganduje-Ajimobi, diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta ce cin zarafin ta da wasu ke yi a yanar gizo ba zai taba razanar da ita ba.

Kada a manta a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta ne Fatima tayi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, inda tace "Na yi dana- sanin zabar shugabanni marasa kishin kasa."

Bayan ta yi wannan wallafar ne da wasu awanni, sai gashi ta kara wata, inda tace, "Shiru ma magana ce."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel