Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya (Bidiyo)

Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya (Bidiyo)

- Mutane a jihar Kwara sun tafi dakin ajiyar kaya sun kwashi kayan abincin tallafin korona

- Bidiyon ya nuna mutane maza da mata suna ta gaggawar shiga dakin ajiyar kayan abinci

- An kuma hasko wasu daga cikinsu suna fitowa da kayan abinci a hannunsu da buhunna a kansu

Wasu mutane a jihar Kwara sun afka dakin ajiya kayayyaki da ke layin Airport road a Ilorin inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so.

Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a cikin motocci, babura da wasu ababen hawan.

Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya (Bidiyo)
Mazauna Kwara suna diban kayan abinci na korona. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan da wasu mutanen a jihar Osun suka yi kutse a wani dakin ajiye kaya a Ede suna kwashi kayan abincin zuwa gidajensu.

A wani labarin, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita na awa 24 da aka saka a jihar a lokacin da rikici ya yi kamari a jihar sakamakon zanga zangar EndSARS.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne yayin wata jawabi da ya yi a ranar Juma'a.

Da ya ke jawabi bayan ya ziyarci wuraren da aka yi rikici a jihar, gwamnan ya ce daga ranar Asabar mutane suna iya fita daga karfe 8 na safe zuwa karfe shida na yamma.

Ya ce za a sake yin bita kan dokar hana fitar a ranar Litinin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya ce bai taba ganin barna irin wanda aka yi cikin 'yan kwanakin nan ba a tarihin jihar Legas.

Amma duk da haka ya mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi don farfadowa da kawo gyara a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164