Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Zamfara

- Matawalle ya ce rusa rundunar SARS matsala ne ga al'ummar jiharsa

- Ya bukaci a kara tura jami'an tsaro jihar domin kawar da yan bindiga

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, a ranar Juma'a ya bayyana cewa sama da yan kasar waje 31 aka kora daga Najeriya saboda hakan ma'adinai ba bisa doka ba a jihar.

Gwamna ya kara da cewa mutane 20 yan bindiga suka kashe ranar Laraba bayan rusa rundunar SARS da gwamnatin tarayya tayi, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnat Matawalle ya bayyana hakan ne ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari inda ya bukaci a dawo masa da jami'an SARS.

Ya kawo wa shugaba Buhari ziyara ne kan lamarin tsaron jihar.

"Na zo ne domin bayyanawa shugaban kasa halin da jihar ke ciki. Bayan rusa rundunar SARS mun fuskanci wasu matsaloli, musamman shekaran jiya (Laraba) inda aka kashe mutane 20 a karamar hukumar Talata Mafara, " Matwalle yace

"Saboda haka na bukaci shugaban kasa ya kawo dauki don ganin yadda za'a tura jami'an tsaro kare mana jihar."

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)
Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna) Credit: @Buharisallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Iju-Ishaga

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)
Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna) Credit: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna)
Kisan mutane 20: Matawalle ya kaiwa Buhari kuka Villa (Hotuna) Credit: @Buharisallau1
Asali: Twitter

DUBA NAN: Harbe-harben Lekki: Hedkwatar Tsaro ta yi martani, ta ce kirkirar bidiyon aka yi

Mun kawo muku cewa yan bindiga sun hallaka akalla mutane 22 a garin Tungar Kwana dake karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar Zamfara daren Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.

Wani dan garin, Malam Ahmed Mohammed ya bayyanawa wakilin Punch cewa yan bindiga sama da 100 sun kai farmako kauyen misalin karfe 11 na dare kuma suka fara harbe-harbe.

Yace: "Mutane ashirin da biyu, wanda ya hada da mata da yara aka kashe lokaci guda, yayinda wasu suka gudu cikin daji."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel