An sallami 'yan sanda shida daga aiki a Kwara

An sallami 'yan sanda shida daga aiki a Kwara

- Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kwara ta ce ta salami jami'an ta shida da aka samu da aikata laifuka da suka saba dokar aiki

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Kayode Egbetokun ne ya sanar da hakan yayin wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki kan tsaro da kungiyoyi a jihar

- Egbetokun ya bukaci kungiyoyin su gargadi mambobinsu su guji kwaikwayon zanga zangar da aka yi a wasu jihohi na EndSARs don bata gari sun lalata abin

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa an kori jami'ai shida daga aiki a jihar kan wasu laifuka da aka ce sun aikata da suka saba wa dokar aiki kamar yadda LIB ta ruwaito.

Shugaban 'yan sandan ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki tare da shugabanin kungiyar direbobi ta kasa, NURTW da RTEAN da kungiyar masu adai-daita sahu, TOAN, masu otel, 'yan acaba, shugabannin dalibai da masu kare hakkin bil adama a jihar.

An sallami 'yan sanda shida daga aiki a Kwara
'Yan sandan Najeriya. Hoto daga @lindaikeji
Asali: UGC

DUBA WANNAN: EndSARS: Adesina ya dora laifi kan masallatai da coci-coci

Egbetokun ya ce an hukunta 'yan sanda da dama ya kara da cewa batun cin zali da karbar na garo da wasu 'yan sanda ke yi ya ragu sosai a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan na Kwara ya kuma bayyana ba su samu batun kisa ba tare da shari'a ba, cin zarafi da razana mutane a jihar.

Ya ce, "Don Allah ku yi wa mutanen ku magana kada su kwaikwayi abinda ke faruwa a wasu sassan kasar da ya haifar da rashin tsaro. Kamar yadda ku ke ganin yanzu lamarin ba zanga zangar EndSARS bane duba da sata da lalata kayayyaki da ake yi a wasu sassan kasar. Akwai alamar abin ya rikide ya zama makircin wasu bata gari.

KU KARANTA: Gwamna Wike ya saka dokar hana fita a wasu kananan hukumomi

"Suna zuwa wurin ajiyar makamai da bindigu domin suna sace makamai domin daga baya su aikata laifuka da su. Kamata ya yi muyi gargadi game da lamarin mu kuma dinga takatsantsan da irin labaran da muke gani a dandalin sada zumunta. Labaran karya na iya kawo rabuwar kai da tashin hankali. Sai mun kula."

A wani rahoton, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello a ranar Laraba ya kira taron tsaro na gaggawa a kan zanga zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ministan a jawabinsa na bude taro ya ce an kira taron ne, "Don bita kan abubuwan firgici da suka faru cikin mako daya da ya gabata" da nufin tabbatar da ganin lamura sun koma yadda suke a baya a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel