EndSARS: Abdulsalami Abubakar ya bukaci matasa su rungumi zaman lafiya

EndSARS: Abdulsalami Abubakar ya bukaci matasa su rungumi zaman lafiya

-Abdulsalami ya bayyana cewa rashin kawo karshen zanga zangar #ENDSARS ka iya kawo wa Najeriya koma baya

-Abdussalami ya shawarci matasa da su rungumi sulhu a matsayin hanyar warware matsaloinsu

-Ya bayyana rashin jin dadi akan yadda bata gari suka lalata kayan gwamnati da sunan zanga zanga

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (ritaya) ya yi kira ga matasan Najeriya su dakatar da zanga zangar EndSARS don bada daman tattaunawa.

Abdulsalami ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da 'yan jarida a Minna akan zanga zangar #ENDSARS da ake yi a kasar nan.

Yayi bayanin cewa yanayin ya sanya damuwa a zukatan yan kishin kasa da dama, kuma yayi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba zai iya janyo wa Kasar nan koma bayan da ya wuce tsammani.

DUBA WANNAN: Babu gwamnatin da kai tamu yaƙar talauci, in ji Buhari

Abdulsalami Abubakar ya bukaci matasa su rungumi zaman lafiya
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Abdulsalami Abubakar. Hoto daga Nigerian Tribune
Asali: UGC

KU KARANTA: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Tsohon shugaban Kasar ya shawarci matasa, wanda suka bayyana kudirinsu da bukatunsu, da su daina zanga zangar su kuma zauna domin ayi sulhu.

Ya kuma shawarci shugaba Buhari da ya tabbatar an biyawa masu zanga zangar bukatunsu.

Ya bayyana rashin jin dadinsa ganin yadda bata gari suka dinga farfasa da kona kayyakin gwamnati dana daidaikun mutane tare da balle fursunoni.

Abdussalami yace wannan ya tilastawa gwamnati tura jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya, sai dai hakan ya janyo mutuwar rayukan wanda basu jiba basu gani ba.

A wani rahoton daban, ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello a ranar Laraba ya kira taron tsaro na gaggawa a kan zanga zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ministan a jawabinsa na bude taro ya ce an kira taron ne, "Don bita kan abubuwan firgici da suka faru cikin mako daya da ya gabata" da nufin tabbatar da ganin lamura sun koma yadda suke a baya a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel