Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya

- Shugaban kasa ya kira taron gaggawa na tsofin shugabannin Najeriya

- Kusan duka tsafin shugabannin sun shiga ganawar ta yanar gizo

- Wannan ya biyo bayan jawabin da shugaban kasan ya yi ga kasa a daren Alhamis

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga taron gaggawa da wasu tsofin shugabannin Najeriya da hafsoshin tsaro.

Duk da cewa ba'a bayyana ainihin dalilin ganawar ba, ana kyautata zaton taron da aka shiga misalin karfe 10 na safe kan abubuwan da ke faruwa a sassan Najeriya.

Dukkan tsofaffin shugaban Najeriya na Soja da Demokradiyya na hallare ta yanar gizo yayinda hafsoshin tsaro da ministoci ke hallare a cikin fadar shugaban kasa.

Daga cikin tsofaffin shugabannin kasa dake hallare sune Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Abdulsalami Abubakar (Rtd), Goodluck Jonathan da Chief Ernest Shonekan.

Wadanda ke hallare a fadar shugaban aksa sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; sakataren gwamnati, Boss Mustapha; Farfesa Ibrahim Gambari da NSA Babagana Monguno.

Sauran sune shugaban hafsoshin tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; IG na yan sanda, Mohammed Adamu; dirakta janar na DSS, Yusuf Bichi da diraktan NIA, Ahmed Rufa'i.

KU KARANTA: Akalla Ofishohin yan sanda 17 bata gari suka kona a Legas - Kaakin hukumar

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga taron gaggawa da tsaffin shugabannin Najeriya
Asali: Twitter

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da duk wani zanga-zanga a fadin tarayya.

A jawabin da yayi a daren Alhamis, ya ce ya dakatad da zanga-zanga ne saboda yadda rajin #EndSARS ya canza zani a fadin tarayya, kuma yan baranda sun kwace abin.

Shugaban kasan yace: "Saboda haka ina kira ga matasanmu su daina zanga-zanga kuma su shiga tattaunawa da gwamnati wajen neman mafita."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel