EndSARS: Adesina ya dora laifi kan masallatai da coci-coci

EndSARS: Adesina ya dora laifi kan masallatai da coci-coci

- Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina ya ce wasu masallatai da coci-coci sun mayar da kansu cibiyoyin watsa sakon kiyayya

- Femi Adesina ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa game da zanga zangar EndSARS da matasa suka yi na neman soke rundunar 'yan sandan SARS

- Ya ce wasu cibiyoyin addinin sun bari masu wata manufa daban suna amfani da su don raba kan al'umma da wanzar da kiyayya

Mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa kan kafar watsa labarai, Femi Adesina ya ce wasu masallatai da coci-coci da wasu kafafen baza labarai na kiyayya.

Ya kara da cewa zanga zangar EndSARS wata dama ce da wasu suke amfani da ita don watsa sakonnin kiyayya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

EndSARS: Adesina ya dora laifi kan masallatai da coci-coci
Femi Adesina. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Kakakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa mai taken, 'Idan Najeriya ta mutu, Kiyayya ne ya kashe ta'.

DUBA WANNAN: Babu gwamnatin da kai tamu yaƙar talauci, in ji Buhari

Adesina ya rubuta, "An fara zanga-zangar EndSARS ne don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda da nufi guda daya. Kwatsam, sai abin ya juya ya zama kafar watsa sakonnin kiyayya a kan shugabanni, a kan hadin kan kasa, ya zama wani kafa na cimma burin siyasa da neman kwace mulki a 2023. Kiyayya ya shiga lamarin."

Wasu daga cikin malaman addini kamar shugaban cocin, Redeemed Christian Church of God, Fasto Enoch Adeboye ya nuna goyon bayansa karara ga zanga-zangar ta EndSARS har cocin ta wallafa bidiyon wasu da suka ce 'yan sanda sun zalunce su.

Duk da haka, Adesina ya ce masallatai da coci-coci sun yi amfani da zanga zangar don yada sakon kiyayya da raba kan al'umma.

KU KARANTA: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Mai magana da yawun shugaban kasar ya cigaba da yin bayyanai kan yadda zanga zangar da matasar ke yi na ganin an samu sauyi kan yadda 'yan sanda ke aikinsu zuwa neman shugaban kasa ya yi murabus daga mukaminsa.

Ya ce masu neman ganin Najeriya ta rabu sun shiga rigar masu zanga zangar suna yada manufarsu don ganin kasar ta tarwatse.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel