Akalla Ofishohin yan sanda 17 bata gari suka kona a Legas - Kaakin hukumar

Akalla Ofishohin yan sanda 17 bata gari suka kona a Legas - Kaakin hukumar

- Zanga-zangar EndSARS ta canza zani fadin tarayya musamman jihar Legas da Abuja

- Masu sharhi sun bayyana cewa yan siyasa suka tura bata gari don lalata dukiyoyin gwamnati

- An yi asarar jamian yan sanda da dama da kuma mata

Hukumar yan sanda a jihar Lagos ranar Juma'a, ta yi gargadin cewa kone-konen ofishohin yan sandan da ake yi zai haifar da koma baya ga al'ummar jihar da kuma zuba kudi wajen sake ginasu maimakon wasu ayyukan amfani daban.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Olumuyiwa Adejobi, ya yi gargadin a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

Ya ce sama da tashohon yan sanda 17 a fadin jihar da bata gari suka lalata gaba daya.

KU KARANTA: EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa

"Illan abin shine kudin da aka shirya amfani da shi wajen wasu ayyuka da cigaban gari za'a karkatar wajen gyaran ofishohin da aka lalata."

"Hakazalika aikinmu yanzu zai kara wuya saboda zamu kara adadin sintiri domin kiyaye wuraren da asali ofishohin nan ya kamata ayi amfani."

"Ban da tabbacin wasu ofishohin dake cikin unguwanni zasu iya kara aiki kamar yadda sukeyi saboda irin asarar motoci da kwamfutoci da aka yi, " Kakakin yace.

DUBA NAN: Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya

Akalla Ofishohin yan sanda 17 bata gari suka kona a Legas - Kaakin hukumar
Akalla Ofishohin yan sanda 17 bata gari suka kona a Legas - Kaakin hukumar Credit: Vanguard
Asali: Twitter

A jiya mun kawo muku cewa ofishin yan sanda sama da 10 aka kona.

Kakakin yace: "Bata gari, wadanda suke cigaba da tayar da tarzoma a jihar Legas da sunan zanga-zangar #EndSARS, sun kashe yan sanda biyu a ofishin yan sandan Orile, sun jikkata da dama kuma sun kona ofishohin yan sanda 10 a jihar."

"Daga cikin ofishohin yan sandan da aka kai hari akwai na unguwannin Idimu, Igando, Layeni, Denton, Ilenbe Hausa, Ajah, Amukoko, Ilasa, Cele Outpost under Ijesha, ofishin SARS dake Ajegunle, Ebute-Ero Mushin (Olosan), Ojo da Ajegunle."

Adejobi ya kara cewa hukumar ta samu rahotanni daban-daban na bata gari dake kai hare-hare gidajen mutane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel