Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Iju-Ishaga

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Iju-Ishaga

- Da alamun an fara rikicin kabilanci a karamar hukumar Iju ta jihar Legas

- Matasa bata gari sun kai hare-hare kamfanoni da shagunan mutane ranar Alhamis

Ana rikici yanzu haka tsakanin Hausawa da Yarabawa a Fagba, Iju-Ishaga, karamar hukumar Ifako-Ijaye inda aka kona gidajen mutane kuma hankulan mazauna sun tashi, cewar Vanguard.

Har yanzu babu jami'an tsaron da suka je kuma ba'a adadin wadanda abin ya shafa ba tukun.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, ya tabbatar da hakan kuma ya yi kira ga shugabannin garin su yiwa matasans magana.

Ya ce ita kanta hukumar yan sandan na fuskantar matsala.

"Akwai dokar hana fita kuma kowa ya koma gida. Aiki ya yiwa yan sanda yawa, mu hada kai domin kawo karshen lamarin," Kakakin yace.

KU KARANTA: Harbe-harben Lekki: Hedkwatar Tsaro ta yi martani, ta ce kirkirar bidiyon aka yi

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Iju-Ishaga
Yanzu-yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Iju-Ishaga Hoto
Asali: UGC

Daya daga mazauna yankin, Aina, ya bayyanawa The Punch cewa "Mun kasa fita daga gudajenmu. Tun ranar Talata suka fara fada. Mun yi tunanin abin ya tsaya jiya ne amma suka cigaba yau."

"Ban san abinda ya janyo fadan ba, kawai na ga mutane na ta guje-guje."

KU KARANTA: Jan-kunne, a koma-aiki, sabon albashi da sauran abubuwan da Buhari ya fada

A bangare guda, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa kan kafar watsa labarai, Femi Adesina ya ce wasu masallatai da coci-coci da wasu kafafen baza labarai na kiyayya.

Ya kara da cewa zanga zangar EndSARS wata dama ce da wasu suke amfani da ita don watsa sakonnin kiyayya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel