Babu gwamnatin da kai tamu yaƙar talauci, in ji Buhari

Babu gwamnatin da kai tamu yaƙar talauci, in ji Buhari

- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wata gwamnati data fito da tsarikan yaƙar talauci kamar tasa

- Buhari ya shawarci masu zanga zanga da kada su bari ɓata gari suyi amfani dasu wajen lalata kyakkwawan tsarin dimokradiyya

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa naira biliyan 75 don samar da ayyukan yi da dama ga matasa

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa kokarin yaƙar talauci zahiri da badini. Buhari ya bayyana hakan a jawabin kai tsaye da ya yi wa 'yan kasa a daren ranar Alhamis.

Acewarsa gwamnatinsa ta dauki matakai da ƙirƙirar tsare-tsare wanda akayi musamman don cigaban matasa, mata da wanda abin ya shafa a cikin al'umma.

Babu gwamnatin da kai tamu yaƙar talauci - Shugaba Buhari
Muhammadu Buhari. Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Ya ce, "Wannan na daga cikin babban tsarin mu na ceto y'an Najeriya miliyan 100 daga k'angin talauci nan shekaru 10 masu zuwa.

"Mun ƙirƙiri hannun jari na naira biliyan 75 don samar da damammaki ga matasa da masu k'ananan da matsaikaita masana'antu (MSME) wanda aka fi sani da survival fund.

"Biyan kuɗin albashin wata uku na ma'aikata dubu 100, na ƙanana da matsakaitan masana'antu, biyan kudin rijistar CAC ga mutane dubu 250 da makamantansu.

"Wannan ƙari ne akan tsaruka irinsu; Farmer moni, Tradermoni, Marketmoni, N-power, N-Tech da N-Agro."

KU KARANTA: Wasu 'yan Najeriya sunyi zaton rushe SARS da muka yi ragwanci ne - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi kira ga masu zanga zangar da suyi tunani akan irin kokarin da yake na inganta rayuwar matasa irinsu.

"A wannan yanayin nake kira ga masu zanga zanga da suyi amfani da irin tunanin da muke na inganta rayuwarsu, su kuma sauke fushi tare da kaucewa bata gari wajen yin amfani dasu don kawo hayaniya da haddasa fitina da nufin lalata tsarin damokradiyya," a cewarsa.

A wani labarin daban, Kotu a Ebonyi da ke zamanta a Abakalili, a ranar Laraba ta bada umarnin tsare wasu mutum hudu da ake zargi da hannu wajen kai hari ga shugaban 'yan sanda na Ohaukwu tare da sace bindigun kananan 'yan sandan yankin.

Waɗanda ake zargin, Okochukwu Onwe, mai shekara 23; Onyedikachi Onwe, mai shekara 22; Chinonso Agbo, mai shekara 25; da kuma Aliezie Uchenna mai shekara 33, ana zargin sun saci bindigu biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel