Harbe-harben Lekki: Hedkwatar Tsaro ta yi martani, ta ce kirkirar bidiyon aka yi

Harbe-harben Lekki: Hedkwatar Tsaro ta yi martani, ta ce kirkirar bidiyon aka yi

- Hedikwatar tsaro ta karyata bidiyon harbin masu zanga zanga a Lekki Toll Gate

- Wasu daga cikin masu zanga zangar #EndSARS sun rasa rayukansu a hadarin daya faru ranar talata

- Manjo Janar, John Eneche, mai kula da yada labaran hedikwatar tsaro ya ce bidiyon harbin an ƙage shi ne

Babbar hedikwatar tsaro ta Najeriya tayi magana akan zargin harbin wasu daga cikin masu zanga zangar #ENDSARS a Lekki da sojoji sukayi.

PM News ta ruwaito cewa mai kula da yada labaran hedikwatar tsaron Manjo Janar John Eneche, ya bayyana cewa bidiyon da yake yawo a kafafen sadarwa ƙagagge ne, wasu bata gari ne suka hada shi.

Harbe-harben Lekki: Hedkwatar Tsaro ta yi martani, ta ce kirkirar bidiyon aka yi
Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar John Enenche. Hoto daga PM News
Asali: UGC

Kafar sadarwar intanet din, ta rawaito cewa, Eneche ya bayyana cewa rundunar soji tana aikin ne saboda tabbatar da zaman lafiya ya kuma ce sun dakatar da "Operation MESA" a jihohi guda tara.

Ya yi kuma bayani akan jami'an tsaron hadin gwiwa, ya bayyana cewa "Operation MESA" yana karkashin kulawar gwamnatin jihohi kuma ya ƙunshi sojojin sama , sojojin ruwa, jami'an Civil Defense da na 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Ya ce: "Lamarin bani da ikon cewa komai akansa, amma ina tabbatar muku da cewa ƙage ne, bai kamata mu fara daukar mataki akan abun da bamu da tabbashi ba.

"Inda ace har yanzu ana maganar batun ne da sai in muku ƙarin bayani, amma bayan faruwar lamarin da awanni kadan gwamna Sanwo-Olu yayi wa al'umma jawabi.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon matasa na kwasar kayan tallafin korona a Legas

"Saboda haka duk abin da zamu fada yanzu zai zama rashin adalci."

Waɗannan jami'an haɗin gwiwar suna ci gaba da aiki kuma na tabbatar gwamnatin jihohi suna amfani dasu ta hanyar data dace.

"Wannan yanayin ya sanya hukumar yan sanda tura jami'an daya kamata su kula da rikicin."

A wani labarin, shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga Shugaba Buhari da yin sulhu da masu zanga-zangar #ENDSARS.

Ya yi gargadin cewa rikici bashi zai kawo karshen matsalar zanga zangar da ake don nuna bacin rai kan muguntar yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel