Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya

Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya

- Bayan kwanaki ana sauraron jawabin Buhari, ya ci magana na tsawon mintuna 12

- Buhari ya yi kira ga matasa su tsagaita zanga-zanga a fadin tarayya

- Yan Najeriya da dama sun yi tsokaci kan jawabin da Buhari yayi

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da duk wani zanga-zanga a fadin tarayya.

A jawabin da yayi a daren Alhamis, ya ce ya dakatad da zanga-zanga ne saboda yadda rajin #EndSARS ya canza zani a fadin tarayya, kuma yan baranda sun kwace abin.

Shugaban kasan yace: "Saboda haka ina kira ga matasanmu su daina zanga-zanga kuma su shiga tattaunawa da gwamnati wajen neman mafita."

"Mun saurareku sosai kuma muna dubawa."

Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya
Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya Credit: @BuhariSallau1
Asali: Twitter

DUBA NAN: EndSARS: Wasu bata gari na kokarin juyin mulki amma ba zamu yarda ba - Gwamnonin Arewa

A cigaba da jawabinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce wasu 'yan Najeriya suna zaton ragwanci ne gaggawar da gwamnati ta yi na soke rundunar 'yan sanda ta musamman masu yaki da fashi da makami na SARS.

A jawabin da Buhari ke yi wa 'yan Najeriya a ranar Alhamis, shugaban kasar ya ce, "A matsayin mu na gwamnatin demokradiyya, mun saurari koken mutane da kunnen basira mun kuma yi nazarin bukatunsu masu zanga zangar guda biyar.

Bayan amincewa, nan take muka soke SARS, sannan muka dauki matakan aiki kan sauran bukatun matasan mu.

KU KARANTA: Jerin gidajen yari 5 da aka kai wa hari a yayin zanga-zangar EndSARS

"A kan rushe SARS, na bayyana karara cewa hakan ya dace da tsarin mu na yi wa aikin dan sanda garambawul.

"Abin bakin ciki, akwai alamun gaggawar amsa bukatun da muka yi ya saka wasu na ganin tamkar ragwanci ne hakan yasa wasu marasa kishin kasa suka fara amfani da damar cimma burinsu mara kyau."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel