Sabon tsarin albashin 'yan sanda na zuwa nan babu dadewa - Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canja tsarin biyan albashin jami'an 'yan sanda
- Ya sanar da hakanne a jawabin kai tsaye da yayi da yammacin Alhamis, 22 ga watan Oktoba
- Inda ya umarci hukumar albashi ta kasa da tayi gaggawar amsar sabon tsarin, yayi hakanne don walwalarsu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabon salon biyan albashin jami'an 'yan sanda, inda ya umarci hukumar albashi ta kasa da tayi gaggawar amsar canjin.
Shugaba Buhari ya fadi hakanne a jawabin kai tsaye a ranar Alhamis da yamma.
Buhari yace, "Don tabbatar da jindadi da walwalar 'yan sanda, an umarci hukumar albashi da tayi gaggawar tabbatar da sabon tsarin albashin jami'an 'yan sandan. Ana duba a kan yadda za'a bullo wa albashin sauran jami'an tsaro."
KU KARANTA: Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa kishin kasa - Fatima Ganduje Ajimobi

Asali: Twitter
KU KARANTA: Da duminsa: Jami'an tsaro sun isa fursuna ta Ikoyi bayan yunkurin balle ta
A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan.
Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna.
Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani.
A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame.
"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai," sakon yace.
An umarci dukkan 'yan sanda masu tsaron da aka janye da su gaggauta zuwa gaban kwamandansu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng