Wasu 'yan Najeriya sunyi zaton rushe SARS da muka yi ragwanci ne - Buhari

Wasu 'yan Najeriya sunyi zaton rushe SARS da muka yi ragwanci ne - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi a ranar Alhamis 22 ga watan Oktoba

- Shugaba Buhari ya ce akwai wasu rukunin 'yan Najeriya da ke ganin kamar ragwanci ne gaggawar da gwamnati tayi na soke SARS kamar yadda masu zanga zanga suka nema

- Buhari ya ce soke SARS din ya yi daidai da shirin gwamnatinsa na yi wa rundunar 'yan sandan Najeriya garambawul

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wasu 'yan Najeriya suna zaton ragwanci ne gaggawar da gwamnati ta yi na soke rundunar 'yan sanda ta musamman masu yaki da fashi da makami na SARS.

Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya yi wa kasar kai tsaye a yammacin ranar Alhamis.

Wasu 'yan Najeriya sunyi zaton rushe SARS da muka yi ragwanci ne - Buhari
Shugaba Buhari. Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna da bidiyon matasa na kwasar kayan tallafin korona a Legas

Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya soke rundunar ta SARS a farkon kwanakin da aka fara zanga zangar.

Adamu ya sanar da kafa wata sabuwar rundunar da za ta maye SARS mai suna SWAT.

KU KARANTA: Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

A jawabin da Buhari ke yi wa 'yan Najeriya a ranar Alhamis, shugaban kasar ya ce, "A matsayin mu na gwamnatin demokradiyya, mun saurari koken mutane da kunnen basira mun kuma yi nazarin bukatunsu masu zanga zangar guda biyar. Bayan amincewa, nan take muka soke SARS, sannan muka dauki matakan aiki kan sauran bukatun matasan mu.

"A kan rushe SARS, na bayyana karara cewa hakan ya dace da tsarin mu na yi wa aikin dan sanda garambawul.

"Abin bakin ciki, akwai alamun gaggawar amsa bukatun da muka yi ya saka wasu na ganin tamkar ragwanci ne hakan yasa wasu marasa kishin kasa suka fara amfani da damar cimma burinsu mara kyau."

A wani rahoton, kotu a Ebonyi da ke zamanta a Abakalili, a ranar Laraba ta bada umarnin tsare wasu mutum hudu da ake zargi da hannu wajen kai hari ga shugaban 'yan sanda na Ohaukwu tare da sace bindigun kananan 'yan sandan yankin.

Waɗanda ake zargin, Okochukwu Onwe, mai shekara 23; Onyedikachi Onwe, mai shekara 22; Chinonso Agbo, mai shekara 25; da kuma Aliezie Uchenna mai shekara 33, ana zargin sun saci bindigu biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel