Yanzu-yanzu: Buhari zai yi wa kasa jawabi na musamman da daren nan
- Bayan kiraye-kiraye gareshi yayi magana, Buhari zai yi da daren Alhamis
- Mai bada shawara kan lamuran tsaro ya ce Buhari zai dauki matakai masu muhimmanci
Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya misalin karfe 7 na daren nan, cewar fadar shugaban kasa, Aso Villa da yammacin nan a shafinta na Facebook.
A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya rattafa hannu, Buhari ya samu bayanai daga wajen hukumomin tsaro kan abubuwan da ke faruwa a kasar.
"Bayan samun bayanai daga wajen hafsoshin tsaro kan halin da kasa ke ciki, shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga kasa ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2020 misalin karfe 7," cewar jawabin.

Asali: Original
Abubuwa sun dagule a fadin tarayya tsakanin ranar Talata, 20 ga wata zuwa Alhamis 22 ga watan Oktoba.
Kawo yanzu bata garin matasa sun kai hari gidajen yari domin sakin fursunonin dake cikin. Yayinda suka samu nasara a wasu kuma suka saki fursunoni sama da 2500, Sojoji da yan sanda sun dakile daya na Ikoyi a Legas.
Hakazalika matasa sun kona ofishohin hukumar yan sanda akalla 10 a jihar Legas.
Ga jerin wuraren da aka kaiwa hari:
1. Hukumar kula da tashan jirgin ruwa - An banka wuta
2. Ofishin yan sandan Orile - An banka wuta
3. Garajin Lekki - An banka wuta
4. Tashar Motar BRT dake Oyingbo - An bankawa sabbin motoci wuta
5. Gidan talabijin TVC, Ketu Legas - An banka wuta
6. Ofishin VIO, Ofishin FRSC, Ojodu - An banka wuta
7. Tashar wutan BRT, Ojodu Legas - An banka wuta
8. Tashar BRT dake Berger - An banka wuta
9. Gidan talabijin jihar Legas,Agidingbi, Ikeja - An banka wuta
10. Wajen shakatawa, Oregun, Legas - Agidingbi, Ikeja
11. Fadar Sarkin Legas - An banka wuta
12. Gidan mahaifiyar gwamnan Legas Surulere Legas - An banka wuta
13 Makarantar Kings College
14. Oriental Hotel, Victoria Island Lagos
KU KARANTA: Bata gari sun fasa kurkukun jihar Ondo, sun saki fursunoni 58
15. Sassan bankin AccessBank - An banka wuta
16. Sassan bankin GTBank - An banka wuta
17. Sakatariyan karamar hukumar Ajeromi
18. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Island
19. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Island East
20. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Mainland
21. Sakatariya Ibeju Lekki LCDA
22. Gidan babban yayan gwamnan Legas dake Lagos Island
23. Gidan jaridar The Nation
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng