Yanzu-yanzu: Sojoji, yan sanda na harbe-harbe yayinda matasan ke kokarin fasa gidan yarin Ikoyi a Legas

Yanzu-yanzu: Sojoji, yan sanda na harbe-harbe yayinda matasan ke kokarin fasa gidan yarin Ikoyi a Legas

- Bayan na jihar Edo, batagari na kokarin sakin yan bata gari irinsu dake gidan yarin Ikoyi

- Bidiyoyin da masu idanun shaida suka dauka ya nuna ana gobara da kuma harbe-harbe

- Amma hukumar gidajen yarin ta ce gobara kawai aka yi kuma an kashe wutan

Jami'an yan sanda da Sojoji sun dira gidan gyaran halin a unguwar Ikoyi dake jihar Legas domin dakile yunkurin fitar da fursunoni da wasu bata gari ke yi yanzu haka.

Wani faifan bidiyon da muka samu a kafafen sada zumunta ya nuna hayaki dake tasowa daga cikin gidan yarin yayinda fursunoni ke kokarin guduwa.

The Punch ta ruwaito cewa jami'an hukumar gyaran halin ta sanar da yan sanda da Sojoji da wuri domin kawo musu dauki.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bata gari sun fasa kurkukun jihar Ondo, sun saki fursunoni (Hotuna)

Wakilin Arise TV da ke wajen, Tokunbi Oyetunji, ya ce Sojoji sun fitittiki matasan zuwa wani gida dake Ikeja.

Bata garin na rike da adduna da wasu muggan makamai.

Yanzu-yanzu: Ana artabu tsakanin Sojoji, yan sanda da matasan dake kokarin fasa gidan yarin Ikoyi a Legas
Ikoyi Credit: Punch
Asali: Twitter

Wani mai idon shaida wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa Punch cewa, "Ina iya ganinsu daga saman gida na. Sojoji da yan sanda sun dira wajen. Na ga fursunonin na jifan dutse kuma wuta na ci."

"Jami'an gidan yarin sun taru a kofar shiga gidan yayinda wasu fursunonin sun koma ciki."

DUBA NAN: Bata gari sun sake bankawa gidan jarida mallakin Tinubu, The Nation, wuta

Amma bayan da aka kwantar da kura, jami'an hukumar gyaran hali sun musanta rahoton cewa an yi kokarin fasa kurkuku, sun ce gobara ne kawai.

Kakakin hukumar gidajen gyara halin na jihar Legas, Ritimi Oladokun, ya ce babu bukatan tashin hankali.

Yace: "Gobara aka yi a wani sashen kurkukun kuma an kashe. Babu wani yunkurin fasa gidan yarin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel