Da duminsa: An sake kona ofishin 'yan sanda a Legas

Da duminsa: An sake kona ofishin 'yan sanda a Legas

- Matasa da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun sake banka wa ofishin 'yan sanda wuta a Legas

- Lamarin ya faru ne a ofishin 'yan sanda da ke makarantar Grammar School Ojudu karamar hukumar Ojodu

- 'Yan sandan da ke cikin ofishin sun tsere sannan daga baya wasu 'yan sandan na musamman suka iso suka mamaye ofishin

Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun sake cinna wa ofishin 'yan sanda wuta a Legas kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ofishin 'yan sandan da ke fitaccen makarantar Grammar School Ojudu da ke Ogunnusi road a karamar hukumar Ojodu yana ci da wuta a lokacin da ake hada wannan rahoton.

Da duminsa: An sake kona ofishin 'yan sanda a Legas
'Yan sandan Najeriya. Hoto daga @PulseNigeria247
Asali: Twitter

Rahotanni sun ce 'yan sandan da ke aiki duk sun tsere yayin da 'yan sanda na musamman na Mobile Police sun iso sun zagaye ofishin 'yan sandan.

DUBA WANNAN: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

An hana dukkan mutane da ke kokarin bi ta layin don zuwa Ogba, Agege, da Ikeja an ce su koma.

'Yan sandan na Mobile Police sun rika harba bindiga a iska domin tsoratar da mutane su dena kusantar wurin kamar yadda rahoto ya bayyana.

KU KARANTA: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa an kone ofisoshin 'yan sanda da dama sun fara zanga zangar ta EndSARS musamman tun bayan harbe harben da aka yi a Lekki Toll Gate a daren ranar Talata.

A wani labarin daban, 'Yan daba sun kai hari kan dakin da aka ajiye kayayyakin tallafin korona ranar Alhamis a yankin Mazamaza da ke karamar hukumar Oriade a jahar Lagos.

Bayan da suka samu damar shiga dakin adana kayan, sun kwashe wasu daga cikin kayayyakin tallafin Corona, kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel