Hotuna da bidiyon matasa na kwasar kayan tallafin korona a Legas

Hotuna da bidiyon matasa na kwasar kayan tallafin korona a Legas

- Matasa da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari wani dakin ajiyar kayan tallafin korona a Legas

- Lamarin ya faru ne misalin karfe na safe kamar yadda wani ganau ya bayyana

- Bayan 'yan daban sun kwashi wasu daga cikin kayan abincin, sun kira mutanen unguwa sun ce suma su diba abinda suke so

'Yan daba sun kai hari kan dakin da aka ajiye kayayyakin tallafin Corona ranar Alhamis a yankin Mazamaza da ke karamar hukumar Oriade a jahar Lagos.

Bayan da suka samu damar shiga dakin adana kayan, sun kwashe wasu daga cikin kayayyakin tallafin Corona, kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana.

Hotuna da bidiyon matasa na diban kayan tallafin korona a Legas
Hotunan matasa na diban kayan tallafin korona. Hoto: Amuwo Odofin/ @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

Hotuna da bidiyon matasa na diban kayan tallafin korona a Legas
Hotunan matasa na diban kayan tallafin korona. Hoto: Amuwo Odofin/ @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

Ma'ajiyar kayayyakin tana layin Benster Crescent, wanda akafi kira Monkey Village kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne da misalin 8:00 na safe.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kunna wuta a wata mahada wadda ba nisa daga Ma'ajiyar.

Daga bisani maharan sun bawa mazauna yankin umarnin shiga don diban kayan da aka ajiye.

Wani mazaunin yankin, Sherif Olaiya ya ce, "mun jiyo karar harbe harben bindiga. Maharan sun kai hari kan dakin adana kaya inda anan aka adana kayayyakin tallafin Corona. Suka kuma umarci jama'a da su zo su kwashi kayan."

Da aka tambaye su ya akayi su kasan kayan tallafin Corona ne, sai yace, "An rubuta a jiki".

A wani labarin daban, Kotu a Ebonyi da ke zamanta a Abakalili, a ranar Laraba ta bada umarnin tsare wasu mutum hudu da ake zargi da hannu wajen kai hari ga shugaban 'yan sanda na Ohaukwu tare da sace bindigun kananan 'yan sandan yankin.

Waɗanda ake zargin, Okochukwu Onwe, mai shekara 23; Onyedikachi Onwe, mai shekara 22; Chinonso Agbo, mai shekara 25; da kuma Aliezie Uchenna mai shekara 33, ana zargin sun saci bindigu biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel