Kotu ta bada umurnin tsare mutum 4 da suka yi wa 'yan sanda duka suka kwace bindigarsu

Kotu ta bada umurnin tsare mutum 4 da suka yi wa 'yan sanda duka suka kwace bindigarsu

- Masu fafutukar kafa Biafra sun kaiwa 'yan sanda hari a garin Abakaliki na jihar Ebonyi

- Ana zarginsu da aikata laifuka biyar masu alaka da fashi da makami, tada hankalin jama'a da kuma yunkurin kisan kai.

- Kotu ta bada umurnin cigaba da tsare su a gidan gyaran hali sannan ta dage cigaba da sauraron shari'ar

Kotu a Ebonyi da ke zamanta a Abakalili, a ranar Laraba ta bada umarnin tsare wasu mutum hudu da ake zargi da hannu wajen kai hari ga shugaban 'yan sanda na Ohaukwu tare da sace bindigun kananan 'yan sandan yankin.

Waɗanda ake zargin, Okochukwu Onwe, mai shekara 23; Onyedikachi Onwe, mai shekara 22; Chinonso Agbo, mai shekara 25; da kuma Aliezie Uchenna mai shekara 33, ana zargin sun saci bindigu biyu.

Kotu ta bada umurnin tsare mutum 4 da suka yi wa 'yan sanda duka suka kwace bindigarsu
'Yan sandan Najeriya. Hoto daga @PulseNigeria247
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: Na tattauna da Buhari - Shugaban Ghana, Akufo-Addo

Anyi nasarar kama wanda ake zargin bayan haɗin gwiwa tsakanin 'yan sanda da jami'an sintirin yankin wanda sun dade a tsare, a hedikwatar yan sanda ta Ebonyi, Abakalili, kafin gurfanar dasu a ranar Laraba.

The Punch ta ruwaito cewa harin ya faru ne bayan kammala tattaunawa tsakanin jami'an tsaro a hedikwatar 'yan sanda ta yankin Ohaukwu, yankin Ezzamgbo.

"Yan tawayen sun tunkari 'yan sandan ne kamar wanda suka je kai korafi, wanda yasa sukayi amfani da wannan damar suka kai masa hari, suka ƙwaci bindigarsa suka kuma tarwatsa jama'a," kamar yadda majiyar ta shaida.

KU KARANTA: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

'Yan sanda sun tabbatar da cewa maharan 'yan fafutukar kafa Biafra ne.

An dai gurfanar dasu ne bisa zargin fashi da makami, tada hankalin jama'a da kuma yunkurin kisan kai.

Dan sanda mai gabatar da kara ya ce laifukan sun sabawa sashi na 516(a),320 (a) da kuma sashi 402 na kundin manyan laifuka na jihar Ebonyi na 2010.

Sai dai lauyan wanda ake kara F. M Nwebo, ya bukaci a bada su beli.

Lauyan masu kara Mbam ya soki kudurin inda ya ce wanda al'amarin ya afkawa suna can a kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.

Alkalin ya bada umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan kaso tare da mika rahoton su cibiyar sauraren karrakkin jama'a don daukar mataki

A wani rahoton, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello a ranar Laraba ya kira taron tsaro na gaggawa a kan zanga zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ministan a jawabinsa na bude taro ya ce an kira taron ne, "Don bita kan abubuwan firgici da suka faru cikin mako daya da ya gabata" da nufin tabbatar da ganin lamura sun koma yadda suke a baya a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel