Shugaban ƙasa 2023: Jerin sunayen mutane 5 da PDP ta fitar, ɗaya zai gaji Buhari

Shugaban ƙasa 2023: Jerin sunayen mutane 5 da PDP ta fitar, ɗaya zai gaji Buhari

- Jam’iyyar PDP reshen Ebonyi ta yi barazanar sanya kafar wando daya da shugabanninta na kasa idan ba a mika tikitin zaben shugaban kasa na 2023 zuwa yankin kudu maso gabas ba

- Reshen ta bayyana cewa yankin na da kwararrun mutane da za su iya karbar ragamar shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari idan mulkinsa ya kare

- Jam’iyyar ta ambaci tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Peter Obi, masaniyar tattalin arziki, Ngozi Okonjo Iweala a matsayin mutane da suka gogu

Yayinda ake ci gaba da tattaunawa kan 2023, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Ebonyi ta bukaci jam’iyyar da ta mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu maso gabas.

Shugaban PDP a jihar, Onyekachi Nwebonyi, ya yi wannan rokon a yayinda yake jawabi ga manema labarai a Abakaliki a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

Nwebonyi ya yi gargadin cewa za a kwashi yan kallo Idan shugabancin jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Uche Secondus, bata bai wa yankin kudu maso gabas tikitin ba.

Ya bayyana cewa idan shugaban jam’iyyar na kasa ya ki aiwatar da bukatar, hakan zai haifar da rashin jin dadi kuma yana iya dakushe damar PDP na lashe zaben 2023.

KU KARANTA KUMA: Shiru magana ce, caccakata a yanar gizo ba mafita bace - Fatima Ganduje-Ajimobi

Shugaban ƙasa 2023: Jerin sunayen mutane 5 da PDP ta fitar, ɗaya zai gaji Buhari
Shugaban ƙasa 2023: Jerin sunayen mutane 5 da PDP ta fitar, ɗaya zai gaji Buhari Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Shugaban na PDP a Ebonyi ya jadadda cewa mika tikitin shugaban kasa na jam’iyyar zai tabbatar da adalci da daidaito, inda ya kara da cewa za su marawa Secondus baya domin ya zarce.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar

Legit.ng ta lura cewa matsayar PDP na zuwa ne bayan wata kungiyar Igbo (COSEYL) ta jero wasu mutane 10 da ka iya karbar kujerar shugabancin kasar a 2023 a kudu maso gabas.

A cewarsa:

“Muna kira ga kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP da su duba yiwuwar mika shugabancin kasa ga yankin arewa maso gabas. A aikata hakan cikin mako guda tunda INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023.

“Kudu maso gabas na da kwararrun mutane da suka nuna bajinta a gwamnati. Shakka babu, muna da gogaggun masu ilimi a kasar.

“Muna da hazikan mutane irinsu Sanata Ike Ekweremadu, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Sanata Theodore Orbih, Sanata Pius Anyim. Akwai kuma sauran manyan mutane wadanda ke rike da makaman gwamnati a yanzu haka."

A wani labari na daban, Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya karyata rade-radin ke yawo, ya ce sam bai da hannu a zanga-zangar #EndSARS da ake yi.

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi hira a gidan talabijin na Channels TV, inda ya karyata zargin da ake yi masa.

A cewar Bola Ahmed Tinubu, wasu mutane sun je gaban shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, inda su ka kai masa munafuncinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel