Bata gari sun kona ofisoshin yan sanda 10 - Kakakin hukumar yan sanda
- Kakakin hukumar yan sandan jihar Legas ya bayyana adadin ofishohinsu da matasa suka kona
- An yi asarar rayuka da dama tun lokacin da Sojoji suka budewa masu zanga-zanga wuta
- Hakan ya fusata matasa kuma ya ingiza su kai hare-hare ofishohin gwamnati
Hukumar yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa akalla ofishohin yan sanda 10 aka bankawa wuta tun lokacin da bata gari suka kwace zanga-zangar #EndSARS a jihar.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, a jawabin da ya saki jiya ya bayyana yadda matasa suka kai hare-hare jihar.
Ya ce akalla ofishohin yan sanda 10 aka bankawa wuta tun lokacin da aka fara wannan rikici.
Yace: "Bata gari, wadanda suke cigaba da tayar da tarzoma a jihar Legas da sunan zanga-zangar #EndSARS, sun kashe yan sanda biyu a ofishin yan sandan Orile, sun jikkata da dama kuma sun kona ofishohin yan sanda 10 a jihar."
"Daga cikin ofishohin yan sandan da aka kai hari akwai na unguwannin Idimu, Igando, Layeni, Denton, Ilenbe Hausa, Ajah, Amukoko, Ilasa, Cele Outpost under Ijesha, ofishin SARS dake Ajegunle, Ebute-Ero Mushin (Olosan), Ojo da Ajegunle."
KU DUBA: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a

Asali: Twitter
KU KARANTA: Rikicin #EndSARS: Jerin wurare 23 da bata gari suka kai hari ko bankawa wuta
A bangare guda, wasu bata gari sun bankawa hedkwatar gidan jaridar The Nation, mallakin babban jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu, wuta.
Yanzu haka ginin kamfanin dake Matori a jihar Legas na ci da wuta, a cewar rahoton The Cable Hakan ya biyo bayan kona gidan talabijin na TVC, duka mallakin dan siyasan.
Ana kyautata zaton cewa ana kai wadannan hare-haren dukiyoyin Bola Tinubu don manufa ta siyasa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng