Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90m daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa

- Sarkin Ogbomoso ya ki karbar naira miliyan 10 daga cikin naira miliyan 100 da gwamna Seyi Makinde ya yi alkawarin bashi

- An yi alkawarin bada naira miliyan 100 ne don yin gyare-gyare a fadar sarkin sakamakon barnar da bata gari suka yi yayin zanga zangar EndSARS

- Sarkin ya bayyana cewa ainihin mazauna garin maza da mata sun yi alkawarin za su yi wa fadar garambawul

Sarkin Ogbomoso ya ki karbar N90 daga cikin N100m da gwamnan Oyo ya yi alkawarin bashi don gyaran fadarsa
Gwamna Makinde da Sarkin Ogbomoso. Hoto daga Instagram/@seyimakinde, Facebook/@mywovenwords
Asali: Instagram

Sarkin al'ummar Kasar Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewuni III ya ki karbar tallafin Naira miliyan 100 daga gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde.

Gwamnan yace an ware kudin ne don amfani dasu wajen gyara ɓarnar da akayi wa fadar Ogbomoso mai daɗaɗɗen tarihi, wanda yan ta'adda da yan tawaye da suka fake da zanga zangar #ENDSARS suka aikata.

Sai dai, a wata takarda mai dauke da kwanan wata 19 ga Oktoba 2020, da aka aikewa gwamnan, ta nuna cewa kudaden gyaran fadar da aka lalata zasu fito daga hannun al'ummar yanki Ogbomoso tare da miliyan 10 da gwamnan ya riga ya bayar.

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

Sarkin ya yi wa gwamnan godiya amma ya ce babu bukatar ware makuden kudin domin yi masa gyare-gyare a fadarsa.

A cewar My Woven Words, sarkin na Ogbomoso ya ce naira miliyan 10 da aka bashi nan take bayan harin ya wadatar ba sai an ciko masa naira miliyan 90 din ba.

Sarkin ya ce wasu mazauna garin sun yi alkawarin yin gyare-gyaren.

Sai dai sarkin ya bukaci Seyi Makinde ya samar da ayyukan yi ga dimbin matasa da ke zaman banza a jihar.

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

"Ina son amfani da wannan damar don mika godiya ta da na al'umma ta ga mai girma gwamna na alkawarin bada naira miliyan 100 don gyara da garambawul na fada ta sakamakon harin da aka kai tare da bani naira miliyan 10 nan take.

"Amma bayan ziyarar ka wasu daga cikin al'ummar Ogbomoso sun dauki nauyin yin gyare-gyaren fadar har an fara aikin.

"Don haka, babu bukatar bada sauran naira miliyan 90 din," in ji Sarkin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel